in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
GDP na kasar Sin ya karu da kashi 7.4% a farkon watanni ukun bana
2014-04-16 17:35:48 cri

Alkaluman da hukumar kula da kididdiga ta kasar Sin ta fitar a ranar 16 ga wata nan sun yi nuni da cewa, bisa kwarya-kwaryar kidayar da aka yi, ma'aunin tattalin arzikin kasar Sin na GDP, ya kai kudin Sin yuan biliyan dubu 12 da 820 a farkon watanni ukun wannan shekara da muke ciki, adadin da ya karu da kashi 7.4% bisa na makamancin wannan lokaci a bara, kuma karuwar da ta ragu da kashi 0.3% bisa na watanni ukun karshen shekarar 2013 da ta gabata. Mr.Sheng Laiyun, kakakin hukumar ta kididdiga ya ce, tattalin arzikin kasar Sin ya gudana yadda ya kamata a farkon watanni uku na wannan shekara, kuma kasar Sin tana da imani, da kuma kwarewa ta tabbatar da dorewar ci gaban tattalin arzikinta cikin dogon lokaci.

A kwanakin da suka gabata, wasu sassa daban daban sun yi hasashen cewa, karuwar ma'aunin tattalin arziki na GDP zai yi kasa da kashi 7.5%, hasashen da ya tabbata bisa alkaluman da aka samar a yau. Bisa alkaluman da aka samar, ma'aunin tattalin arzikin kasar Sin na GDP ya kai kudin Sin yuan biliyan dubu 12 da 820 a farkon watanni uku na wannan shekara, adadin da ya karu da kashi 7.4% bisa na makamancin wannan lokaci a bara, kuma karuwar da ta ragu da kashi 0.3% bisa na watanni uku na karshen shekarar da 2013, wadda kuma ba ta kai ga kashi 7.5 bisa dari ba. Wato dai matsakaicin karuwar tattalin arzikin da aka yi hasashen za a samu a shekarar nan ta 2014.

A game da dalilin raguwar, kakakin hukumar kula da kididdiga ta kasar Sin, Mr.Sheng Laiyun ya ce, "Dalili na farko shi ne mawuyacin halin da wasu kasashen ketare ke ciki ta fannin tattalin arziki. Wanda aka shiga a bana, inda tattalin arzikin kasar Amurka ya fuskanci matsaloli masu wuya. A dalilin harkokin hada-hadar kudi, wasu kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa sun fara fuskantar matsala wajen fitar da kayayyakinsu zuwa ketare, abin da ka iya jinkirta bunkasuwar tattalin arziki. Na biyu, kasar Sin na cikin wani mataki na daidaita saurin bunkasuwar tattalin arzikinta, da tsarin tattalin arzikinta, haka kuma wani matakin da wasu manufofin da aka fara aiwatarwa a gaba sun fara tasiri, wadanda tabbas za su kawo hasara ta bangaren tattalin arziki. Na uku, a wannan shekara gwamnati ta kara karfin yin watsi da wasu masana'antun da suke amfani da makamashi da yawa, tare da gurbata muhalli, wasu kananan hukumomin sun kara mai da hankali a kan kare muhalli, da samun dorewar ci gaban tattalin arziki, duk da cewa hakan zai iya rage saurin karuwar tattalin arziki."

A farkon watanni uku da suka gabata, mutane fiye da miliyan 3 sun samu guraben aikin yi a birane da garuruwa na kasar Sin, kuma matsakaicin yawan kudin shigar al'ummar kasar Sin ya karu da kashi 8.6%. Kafin wannan, shugabannin kasar ta Sin sun bayyana cewa, muddin aka tabbatar da rashin samun manyan sauye-sauyen ga bunkasuwar tattalin arziki, kuma aka samar da guraben aikin yi ga al'umma yadda ya kamata, lalle za a iya hakuri da samun raguwar saurin bunkasuwar tattalin arziki. To, amma ko kashi 7.4% ya kasance cikin wani yanayin da ya dace, a game da wannan, kakakin ya ce, "A lokacin da ake auna matsayin bunkasuwar tattalin arziki domin ganin ko ya dace da burin da ake da shi na samun saurin bunkasuwarsa, wani abu mai muhimmanci da ya kamata a lura da shi shi ne, guraben aikin yi da aka samar, da kuma kudin shigar al'umma, wadanda in an duba, ana iya cewa tattalin arzikin kasar Sin ya kasance cikin wani yanayin da ya dace, a farkon watanni ukun da suka gabata."

Kakakin ya jaddada cewa, kasar Sin ta shiga wani sabon mataki na daidaita tsarin tattalin arzikinta, don haka, ya kamata a dubi sauye-sauyen da ke faruwa ga tattalin arzikin kasar da idon basira. Kamar yadda ya fada, "Raguwar saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ya shaida yadda kasar ta shiga wani sabon mataki na daidaita tsarin tattalin arzikinta. Na biyu, a sabon matakin da ake ciki, yadda gwamnati ta rage saurin bunkasuwar tattalin arzikinta zai taimaka ga daidaita tsarin tattalin arzikin. Na uku, kashi 7 bisa dari zuwa kashi 8 bisa dari ba kadan ba ne ga bunkasuwar tattalin arziki, wanda in an kirga, za a ga tattalin arzikin kasar Sin na karuwa duk da cewa saurin sa ya ragu."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China