in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guinea-Bissau ta gudanar da zabe cikin fata na dorewar zaman lafiya
2014-04-14 12:32:10 cri

A jiya Lahadi dai ne, aka gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki kasar Guinea -Bissau na farko, tun bayan wani juyin mulki da dakarun sojin kasar ta suka yi a shekara ta 2012. A yayin zaben, masu kada kuri'a fiye da 800,000 ne suka kada kuri'a a cibiyoyi na zabe dake fadin kasar, wacce ke Afrika ta yamma. An gudanar da zaben a bisa wani muradi na ganin an maido da dorewar zaman lafiya a kasar.

Masu kada kuri'a za su zabi shugaban kasa daga 'yan takara 13. Hakazalika za su zabi 'yan majalisar dokokin kasar 102 daga cikin 'yan takara masu neman mukaman majalisa, wadanda jam'iyyun siyasa na kasar 15 suka gabatar.

An samu masu sa ido na kasashen duniya a kan zaben, kimanin 500 wadanda suka zo daga kasashen ketare, don ganin yadda za'a gudanar da zaben, tare da tabbatar da cewar, an ba kowa hakkinsa, da kuma ganin an yi zaben tare da aiki da gaskiya.

Hukumar zabe ta kasar Guinea Bissau ta ce, an fara gudanar da zaben, ba tare da bata wani lokaci ba, kuma a cikin lumana. Hukumar zaben ta kara da cewar, masu kada kuri'a sun fito bila'adadin, yawancinsu ma suna yin zaben ne, a karo na farko a rayuwarsu.

Ita dai MDD, wacce ta kasance tana taimakon Guinea-Bissau wajen maido da zaman lafiya a kasar, tana mai fatan zaben wanda a can baya an sha daga gudanar da shi, zai haifar da gina tsarin doka, da kuma haifar da habbaka da ci gaban tattalin arziki.

A jajibirin zaben, babban sakataren MDD Ban Ki-moon, ya gabatar da kira a kan jama'ar kasar ta Guinea-Bissau, da kuma hukumomin kasar, da su tsaya tsayin daka wajen ganin an gudanar da zaben a cikin lumana da nagarta.

Babban sakataren MDD, a sakon nasa kamin zaben, ya bukaci masu tsayawa takara, da magoya bayan su, da gwamnatin rikon kwarya ta kasar da hukumomin dake gudanar da zaben, game da kungiyoyi na kare hakkin jama'a da kuma al'ummar kasar ta Guinea-Bissau da su zamanto tsintsiya daya madaurin ki daya domin tabbatar da nasarar zaben. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China