in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar NPC za su mai da hankali kan kare muhalli da sauran fannoni masu muhimmanci
2014-03-10 17:50:15 cri

Asabar 9 ga wata, shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC, mista Zhang Dejiang, ya yi bayani a gaban wakilan jama'a kimanin dubu 3 dangane da ayyukan zaunannen kwamiti na majalisar, a ci gaban taron shekara-shekara na majalisar NPC, hukuma mai ikon mulki na koli na kasar Sin.

A jawabinsa, Zhang Dejiang ya nanata cewa, a shekarar da muke ciki, majalisar NPC za ta kara kafa wasu dokokin da za su shafi ayyukan wasu muhimman fannoni, da kara kokarin sa ido, kan gwamnati da manyan hukumomin kasar. Haka zalika, majalisar za ta taka rawa a kokarin tabbatar da adalci da daidaituwa a zaman al'umma, gami da zurfafa gyare-gyaren da ake yi a kasar.

Yayin da wani mazaunin Beijing mai suna Zhuang ya ambaci sabuwar dokar da ta shafi yawon shakatawa, ya ce,

"Da ma a lokacin da muka yi yawon shakatawa, idan mun gamu da matsala ba mu san inda za mu kai kara ba. Amma yanzu mun samu wannan sabuwar doka, wadda za ta taimaka wajen warware matsala, da kokarin kare hakkin jama'a masu yawon shakatawa."

An fara yin amfani da sabuwar dokar yawon shakatawa a watan Oktoban shekarar bara, wadda ta kasance dokar farko da zaunannen kwamitin majalisar NPC ta wannan karo ya zartas. Bisa wannan dokar an samu damar warware wasu matsalolin da suka hada da sayar da tikitin shiga wuraren yawon shakatawa a kan farashi mai tsada sosai, da tilastawa jama'a sayen kayayyaki da wasu ma'aikata masu kula da ayyukan shakatawa suka yi, lamarin da ya sanya jama'a farin ciki.

Shekarar bara ta kasance shekara ta farko da zaunannen kwamitin majalisar NPC ta 12 ya yi aikinsa. Yayin da yake waiwayar ayyukan kwamitin a shekarar da ta gabata, mista Zhang ya ce,

"Za a tabbatar da matsayin jama'a na masu kasa, da kokarin kyautata tsarin dimokuradiya don ya shafi jama'a da dama tare da sanya jama'a su samu damar gudanar da mulkin kasa bisa majalisar NPC. Za a kuma yi kokarin aiwatar da mulkin kasa bisa doka, da kare karfin tsarin mulki da dokokin kasar, don nuna amfanin majalisar NPC a kokarin gina wata kasa mai bin tsarin gurguzu da martabar dokoki."

A shekarar da ta wuce, dokoki da kudurori da yawa da zaunannen kwamitin majalisar NPC ya zartas sun janyo hankulan jama'a sosai, ga misalin ya gyara dokar kare hakkin masu sayen kayayyaki, da soke dokar tilastawa fursunoni ayyukan kwadago, da kurdurin da aka zartas na kebe ranar tunawa da nasarar jama'ar kasar Sin a yakin kin harin Japan, da dai sauransu. Majalisar ta samu yabo bisa kokarinta na mayar da martani ga bukatun jama'a, da ba da tabbaci ga gyare-gyaren manufofin kasar, da samar da dokoki masu inganci da daidaituwa.

A dayan bangaren kuma, bisa matsayinta na babban ofishin hukumar kasar mai ikon mulki na koli, zaunannen kwamitin majalisar NPC ya yi kokarin sanya ido kan yadda gwamnati da wasu manyan hukumomin kasar Sin suke gudanar da ayyukansu a shekarar bara. Ayyukan da kwamitin ya yi sun shafi duba yadda gwamnatin take amfani da kasafin kudi, da rahoton da gwamnatin ta gabatar kan ayyukan kara gina birane, da tantance yanayin aikin taimakawa masu fama da talauci a kauyuka, da dai makamantansu, wadanda yawancinsu suka shafi zaman rayuwar jama'a. Sa'an nan, game da batun yakar cin hanci da rashawa, zaunannen kwamitin majalisar NPC ya kara kokarin sa ido kan manyan jami'an gwamnati.

Shekarar 2014 da muke ciki ta kasance shekara ta farko da kasar Sin ta fara kokarin zurfafa gyare-gyarenta a gida, kuma ta kasance zagayowar shekarar 60 da aka kafa majalisar NPC, don haka, yadda majalisar za ta tsara ayyukanta a wannan shekara ta kasance cikin batutuwan da suke janyo hankalin jama'ar kasar. A cewar mista Zhang Dejiang, majalisarsa za ta kara kokarin kafa wasu dokoki da suka shafi muhimman ayyuka, da sa ido kan gwamnati da manyan hukumomin kasar. Zhang ya ce,

"Ya kamata zaunannen kwamtinmu na majalisar NPC ya yi kokarin kula da aikin kafa dokoki gami da aiki na aiwatar da gyare-gyare a kasar, don tsara yawan dokoki da suka shafi gyare-gyaren manufofin gwamnati da ake yi a kasar Sin."

Hakika bayanin da mista Zhang ya yi a ranar 9 ga wata ya sheda cewa, an yi shirin gyaran dokokin da suka shafi kai kara kan ayyukan gwamnati, kasafin kudi, kare muhalli, ingancin abinci, da dai sauransu, wadanda suka kasance cikin fannonin da gwamnatin kasar Sin ke neman kyautata yanayin da ake ciki, da batutuwan da jama'ar kasar suka fi mai da hankali a kai. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China