in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na da imanin cimma karuwar cinikayyar waje da kashi 7.5 bisa dari
2014-03-07 17:07:26 cri

A ranar 7 ga watan nan ne aka shirya wani taron manema labaru, dangane da tarurrukan nan 2 da ake gudanarwa a nan birnin Beijing, inda ministan kasuwancin Sin Mista Gao Hucheng ya zanta da manema labaru kan batutuwan da suka shafi raya harkokin kasuwanci, da bude kofar kasar Sin ga duniya. Mista Gao ya ce, Sin tana da imanin cimma burin samun karuwar cinikayyar waje da kashi 7.5 bisa dari.

A shekarar 2013, yawan kudaden cinikayyar kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su, da wadanda ta fitar zuwa ketare ya kai dala tiriliyan 4.16, sakamakon haka Sin ta wuce Amurka, ta kuma zama babbar kasa ta farko a duk duniya wajen cinikayyar kayayyaki. Bisa hakan Sin ta zama kasa daya tilo cikin kasashe masu tasowa, da ta shiga cikin manyan kasashen da ke cinikayyar kayayyaki a duk duniya, a cikin shekaru fiye da dari a tarihin duniya.

Da ya tabo batu kan halin da ake ciki dangane da cinikayyar waje da Sin take yi, ministan kasuwanci na Sin Mista Gao Hucheng ya yi imanin cimma burin karuwar cinikayyar waje da kashi 7.5 bisa dari. Ya ce,

'A shekara ta 2014, tattalin arzikin duniya ya ci gaba da farfadowa, wanda hakan ya taimaka wa kasar Sin wajen fitar da kayayyaki zuwa ketare. A cikin gida kuma, da akwai abubuwa biyu da ke taimakawa karuwar cinikayyar waje. Na farko shi ne tun bayan da rikicin kudi ya rutsa da kasashen duniya duniya, kamfanonin Sin da ke cinikayyar waje sun daidaita harkokinsu a cikin gida, sun kuma inganta kwarewarsu wajen samun bunkasuwa. Na biyu, gyare-gyaren da ake yi kan tsarin gwamnati da na kamfanonin sun taimaka, wanda ya kara inganta karfin takara da kamfanonin cinikayyar wajen suke da shi.'

Don gane da rikicin cinikayya kuwa Mista Gao Hucheng ya bayyana cewa, a yayin da Sin ke kara gudanar da harkokin cinikayya da sauran kasashen waje, yawan rikicin cinikayya shi ma ya karu. Ya ba da wani misali, inda ya ce a shekarar da ta wuce, Sin da kungiyar tarayyar Turai wato EU, sun shawo kan rikicin cinikayyar kayayyakin sarrafa makamashin rana a madadin makamashin wutar lantarki, wadanda darajarsu ta wuce kudin Amurka dala biliyan 20.

Ya kara da cewa, bayan da kasar Sin ta zama babbar kasa ta farko wajen cinikayyar kayayyaki a duk duniya, ya kamata ta kara hakuri da irin rikicin da kan faru a yayin cinikayya, ya ce.

'Abin da muka sanya gaba da farko shi ne, yin musanyar ra'ayoyi da samun sulhuntawa, da hadin kai, da neman wata hanyar da za a bi don daidaita rikici tare da samun moriyar juna. Haka kuma muna da burin samun nasara tare da shawo kan matsaloli yadda ya kamata. Bangarorin Sin da Turai dukkanmu mun fahimci cewa, ya kamata mu kara yin musayar ra'ayoyi, da shawarwari yayin rikicin cinikayya, da samun bunkasuwa tare ta hanyar hadin kai tsakanin sassa daban daban da masana'antumu. Ta wannan hanyar da muke bi ne muka daidaita rikicin da ake fuskanta a yanzu da wadanda ka iya faruwa a nan gaba. Game da wannan batu musamman ga kasar Sin a matsayin ta na babbar kasa ta farko a duk duniya, ya kamata mu rike hakan a duk lokacin da aka samu rikicin cinikayya.' (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China