An cimma matsaya guda game da batutuwa da dama yayin taron fira ministocin kasashe mambobin kungiyar SCO
Muhimman Labaru
Firaministan Sin ya yi jawabi a gun taron firayin ministocin kungiyar SCO Firaministan Sin Li Keqiang ya bayyana aniyar kasar Sin, ta ci gaba da kare abubuwan da aka gada na gargajiya, yayin da ake gudanar da sauye-sauye, da tsayawa kan doka, tare da habaka hanyoyin hadin kai, don tinkarar kalubalolin ci gaba...
Rahotanni
An kaddamar da taswirar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen dake tsakiya da gabashin Turai An kaddamar da shirin Bucharest mai kunshe da tsarin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen dake tsakiya da gabashin Turai a jiya Talata, bayan da shugabannin bangarorin biyu, suka tattaunawa sosai kan dangantakar dake tsakanin su. An kaddamar da wannan shiri ne a yayin taron tattaunawa da aka gudanar tsakanin shugabannin kasar Sin, da na kasashe 16 dake tsakiya da gabashin Turai, a kuma karkashin shugabancin firaministan kasar Sin Li Keqiang da har yanzu ke ci gaba da ziyarar aiki a kasar Romania, da hadin gwiwar takwaransa na kasar ta Romania.