• Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na Nijeriya
Muhimman Labaru
• Kamata ya yi kasa da kasa su kara taimakawa kasashen Afirka, in ji firaministan kasar Sin

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce, kamata ya yi kasa da kasa su girmama jama'ar kasashen Afirka wajen kyale su da su daidaita matsaloli da kansu, kuma su kara ba da hakikanin agaji ga kasashen Afirka domin samun ci gaba.

Wane Ne Goodluck Jonathan?

Goodluck Ebele Jonathan An haife shi ne a watan Nuwamba na shekarar 1957 a jihar BAYELSA ta kasar Nijeriya, ya sami digirinsa a fannin ilmin dabbobi a jami'ar Fatakwal ...

Huldar da ke Tsakanin Sin da Nijeriya
Hotuna
More>>
Rahotanni
• An cimma yarjejeniyoyi da dama tsakanin Sin da Nijeriya
A ranar 10 ga wata da yamma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na tarayyar Nijeriya, Goodluck Jonathan, wanda a halin yanzu ke ziyarar aiki a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar ta Sin, ganarwar da aka dauka a matsayin ganawa tsakanin kasar da ta fi yawan al'umma a duniya, da kuma wadda ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka. A ganawar da suka yi ta tsawon sa'a guda, shugabannin kasashen biyu sun yi musayar ra'ayi dangane da yadda za a dada bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen nasu, da ma kasashen Afirka baki daya, inda suka jaddada muhimmancin taimakon juna, da samun ci gaban tare a matsayin burin bai-daya na kasashen biyu
• Hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen Sin da Nijeriya
A ranar 10 ga wata, an shiga rana ta biyu ta ziyarar shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan a kasar Sin, yau ya gana da shugabannin wasu masana'antun kasar Sin don tattaunawa kan hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu. Wakilinmu Bako ya samu damar shiga cikin tawagarsu, yanzu ga karin bayanin da ya kawo mana.
More>>
Labarai Masu Dumi-duminsu
• Shugaban Najeriya ya koma gida bayan ya kammala ziyararsa a kasar Sin 2013-07-12
• Shugaba Goodluck ya taya gidan radiyon kasar Sin Murnar cika shekaru 50 da kafuwar sashin hausa 2013-07-11
• Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya gana da shugaban Nijeriya 2013-07-11
• Kamata ya yi kasa da kasa su kara taimakawa kasashen Afirka, in ji firaministan kasar Sin 2013-07-11
• Kara zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Nijeriya za ta taimaka wajen bunkasa dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka 2013-07-11
• Shugaban Najeriya ya aza harsashin tubalin gina sabon gidan jakadan Najeriya da ke kasar Sin 2013-07-11
• Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na Nijeriya 2013-07-10
• Goodluck Jonathan ya iso birnin Beijing 2013-07-09
• Jihar Borno ta Nijeriya tana fatan inganta hadin gwiwa da kasar Sin wajen aikin gona 2013-07-05
• Kamfanin Sin ya kaddamar da aikin shimfida layin dogo na zamani a Nijeriya 2013-07-05
More>>
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China