Sanya hannu kan wannan yarjejeniya ya biyo bayan wani taron da ya gudana kwanan nan a birnin Rabat, wanda ya samu halartar manyan ofishin ministan tare da tawagar dake kunshe da darektan asusun kayayyakin tarihin kasa da kasa na Afrika, mista Webber Ndoro, darektan kayayyakin tarihi a ofishin ministan al'adun kasar Afrika ta Kudu, Irwin Langeveld da kuma jami'in dake kula da dangantakar kasa da kasa a asusun Afrika, mista Inge Herbert, a cewa wannan sanarwa ta ofishin ministan al'adun kasar Maroco.
A cewar darektan kayayyakin tarihi a ofishin ministan al'adu, Abdellah Alaoui, wannan yarjejeniya tana bude babbar kofa wajen yin musanyar kwarewar Maroco tare da sauran kasashen Afrika, musammun wadanda dake kudu da hamadar Sahara a fannonin karewa da kuma shigar da muhimmancin kayayyakin tarihi da ba da kulawa ga wuraren tarihi na duniya na kungiyar UNESCO. (Maman Ada)