in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen kungiyar SADC sun yi kira da a kafa cibiyoyin adanon bayanai domin yaki da sumogal din kayayyakin tarihi
2012-11-06 10:19:22 cri

An gayyaci kasashen kungiyar SADC kafa wasu cibiyoyin ajiyar bayanai a cikin kasashensu domin tabbatar da sa ido da ba da kulawa wajen samar da yanayin kiyaye da kare kayayyakin tarihinsu da kuma karfafa dangantaka tsakanin hukumomin al'adu domin yaki da sumogal din kayayyakin tarihi.

A yayin wani taron karawa juna sani kan matsalar sumogal ta haramtattar hanya na kayayyakin al'adu ko tarihi a wannan shiyya da aka gudanar a ranar Litinin a birnin Gaborone, jami'in samar da bayanan sirri na manyan laifuffuka dake aiki tare da jami'in kungiyar kasa da kasa ta Interpol Fabrizio Panone ya bayyana cewa, alkaluma na cibiyar ajiyar bayanan kungiyar Interpol kan kayayyakin tarihi da na al'adu da aka sace sun nuna cewa, kafin ranar 31 ga watan Oktoba na shekarar 2012, akwai kayayyaki 40453 da aka sace, kuma a cikinsu kayayyaki 216 sun bace kwatakwata daga nahiyar Afrika.

A cikin wadannan alkaluman na kasashen SADC, kasar Angola ta sanar da bacewar kayayyakin tarihi bakwai, Zimbabwe biyar, Zambia biyar, Bostswana guda, kana kasar Afrika ta Kudu ta bayyana bacewar kayayyaki 66. Sauran kasashen SADC da suka hada da kamar Malawi, Lesotho, Mozambique, Namibia da Swaziland ba su bayyana satar komi ba, in ji mista Panone.

Hakazalika jami'in ya yi kira ga kasashen Afrika da su kafa cibiyoyin ajiyar adanon bayanai a cikin kasashensu da za su taimakawa kungiyar Interpol samun bayanai masu sahihanci bisa kayayyakin tarihi ko na al'adu da suka bata. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China