in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kira taron kungiyar kula da wuraren tarihi na kasa da kasa a birnin Beijing
2012-10-28 17:25:11 cri
An bude taron kwamitin masu ba da shawara da na zartaswa na kungiyar kula da wuraren tarihi na kasa da na kasa wato ICOMOS na shekara ta 2012 yau Lahadi ranar 28 ga wata a birnin Beijing, fadar gwamnatin kasar Sin, inda ya samu halartar wakilai 112 daga kasashe 56.

Liu Yandong, mamba ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin a jawabin ta wajen bikin bude taron, ta bayyana cewa, bana shekara ce ta cikon shekaru 40 da aka daddale yarjejeniyar kiyaye al'adu da abubuwan halittu na gado na duniya. Dangane da hakan ta yi kira ga kasa da kasa da su aiwatar da manufofin yarjejeniyar domin kiyaye abubuwan tarihi na al'adu gaba daya. Haka kuma ya kamata a nuna girmamawa ga al'adun tarihi daban daban don kiyaye ire-irensu. Bugu da kari, kamata ya yi a kyautata kwarewar kiyaye su, a kokarin samun dauwamammen ci gaba ta fuskar kiyaye abubuwan tarihi na al'adu.

An kafa kungiyar ICOMOS ne a shekara ta 1965 a birnin Warsaw, babban birnin kasar Poland, wadda ta kasance kungiyar mai zaman kanta da ta fi ba da tasiri a fannin kiyaye da kyautata wuraren tarihi a duniya, kana mai ba da shawara ga cibiyar kula da abubuwan tarihi na duniya na kungiyar kula da ilmi da kimiyya da al'adu ta MDD wato UNESCO.

Kasar Sin ta shiga kungiyar ICOMOS a shekara ta 1993. Taron kwamitin masu ba da shawara da na zartaswa na kungiyar da a kan shirya bisa shekara-shekara taro ne mafi muhimmanci na kungiyar. Wannan taron na bana zai kai har zuwa ranar 11 ga wata mai zuwa, inda za a kira taron kwamitin kimiyya, da shirya taron bita kan yadda za a gabatar da kayayyakin da ake neman shigar da su jerin sunayen abubuwan tarihi na duniya. Hakazalika, za a shirya taron kara wa juna sani kan yadda za a rage hadarin da bala'u daga indallahi da bil Adama ke kawo wa abubuwan tarihi na al'adu.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China