in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shigar da lambun shan iska na Sangha cikin takardar jerin sunayen kayayyakin gargajiya na kasa da kasa
2012-07-11 15:24:49 cri

Kwanan baya an kira taron kiyaye kayayyakin gargajiya na kasa da kasa na kungiyar UNESCO ta MDD a birnin Saint-Peterburg na kasar Rasha, inda aka shigar da lambun shan iska na Sangla dake kan iyakar kasashen Congo Brazzaville, Kamaru da Afrika ta tsakiya cikin takardar jerin sunayen kayayyakin gargajiya na kasa da kasa.

Wannan lambun shan iska yana arewa maso yammacin kwarin Congo ne, wanda ya kunshi lambuna uku, wato lambun shan iska na Nouabalé Ndoki na kasar Congon Brazzaville, lambun shan iska na Lobeké na kasar Kamaru da lambun shan iska na Zanga na kasar Afrika ta tsakiya.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, a watan Disamba na shekarar 2000, kasashen uku sun sa hannu kan wata yarjejeniya, inda suka amince da kula da lambun shan iska na Sangha cikin hadin kai. Wannan lambu na da fadin eka dubu 750 wanda kuma ya kunshi halittu masu rai iri-iri dake yanki mafi zafi kuma da ruwan sama da yawa.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China