in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya nuna damuwa kan yanayin da ake ciki a arewacin kasar Mali
2012-07-02 10:34:16 cri
Babban sakataren MDD, Ban Ki-Moon ya bayar da sanarwa a ran Lahadi 1 ga watan Yuli, inda ya nuna damuwa sosai kan yanayin tsaro da na jin kai da ake ciki a arewacin kasar Mali, da kuma makabarta guda uku dake tsohon garin Timbuktu da aka barar.

Kungiya mai tsattsauran ra'ayi Islamic Defenders da ta mamaye arewacin kasar Mali a ranar 30 ga watan Yuni ne ta fara lalata tsohon garin Timbuktu da kungiyar UNESCO ta MDD ta mayar da shi a matsayin kayan tarihi na duniya da aka jefa su cikin hadari. A wannan rana kuma, kungiyar UNESCO ta tabbatar da cewa, an lalata makabarta guda uku dake tsohon garin Timbuktu, ciki har da Sidi Mahmoud, Sidi Moctar da kuma Alpha Moya.

A cikin sanarwar da ya bayar, Ban Ki-Moon ya bayyana cewa, babu wani dalilin da za a fake da shi wajen hallaka wadannan kayayyakin tarihi. Ya kuma yi kira ga bangarori daban daban da su sauke nauyin dake kansu wajen kiyayen kayayyakin tarihi na kasar Mali.

Bugu da kari, Ban Ki-Moon ya jaddada cewa, yana goyon bayan kokarin da kungiyoyin ECOWAS, AU, da kasashen dake yankin suke yi na taimakawa gwamnati da jama'ar kasar Mali wajen warware rikicin da ake fuskanta a yanzu ta hanyar yin shawarwari. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China