in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar UNESCO ta yi kira da hana a lalata kayayyakin gargajiya na kasa da kasa
2012-07-01 17:28:38 cri

Ranar 30 ga watan Yuni a birnin Paris hedkwatar kunigyar, babbar direktar kungiyar UNESCO Irina Bokova ta nuna matukar damuwa ga kayayyakin gargajiya dake kudu da Sahara, saboda aka lalata kaburbura na gargajiya uku dake birnin Timbuktu dake da dogon tarihi a kasar Mali. Kuma ta sake yin kira ga bangarori daban-daban dake kasar da su daina bude wuta tsakaninsu.

A wannan rana, an ba da sanarwa cewa, Irina Bokova ta nuna damuwa sosai kan lalata kaburbura na gargajiya uku dake arewacin kasar Mali masu da daraja sosai da aka yi. Kuma ta yi kira da a daina bude wuta domin kiyaye wadannan kayayyakin gargajiya, tare kuma da daukar nauyin dake bisa kansu na kiyaye kayayyakin gargajiya na kasa da kasa.

Bisa labarin da aka bayar a safiyar wannan rana cewa, kungiyoyi masu matsanancin ra'ayi dake mamaye arewacin kasar Mali sun fara lalata kaburbura na gargajiya 16. Wadannan kaburbura na gargajiya 16 dake birnin Timbuktu dake da dogon tarihi na da muhimmanci sosai wajen tabbatar da asalin jama'ar Mali da kiyaye kayayyakin gargajiya na dukkan duniya gaba daya.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China