in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana`antar sarrafa sikari ta kasar Afrika ta Kudu ta yi alkawarin tallafawa sabon shirin samar da makamashi na kasar
2011-11-07 11:33:59 cri

Shugabannin kamfanin sarrafa sukari na kasar Afrika ta Kudu sun ce a shirye suke su bayar da taimako mai yawan gaske wajen sabunta tsarin samar da makamashi a kasar.

To sai dai a cikin wani rahoto da aka karanta a wata tashar rediyon kasar jiya Lahadi da kungiyar manoman rake ta kasar Afrika ta kudu ta bayar, ta jaddada bukatar samun agajin gwamnati kafin a sa ran samun gudumowar kamfanin.

Mr Garreth Sparks wanda shi ne manajan shiyyar Zulu na kungiyar, a cikin rahoton ya kara jadada irin rawar da kamfanin zai taka wajen samar da mai da za a iya amfani da shi domin samar da wuta a masana`antun sarrafa sukari.

A yanzu haka dai gwamnatin kasar ta tsame manoman rake daga cikin masu amfana da shirinta na samar da man fetur daga sirrai.

Mr. Garreth Sparks ya ce zai yi wahala sabuwar kasuwar fasahar samar da mai ta hanyar amfani da sirrai ta kai ga bunkasuwa muddin dai ba a samar da kyakkywan yanayi ga masu zuba jari ba.

Kamfanin kasar Afrika ta Kudu ya gabatar da wannan alkawari nasa ne, makonni uku kafin babban taron MDD wanda za a tattauna a kan batun yanayi da za`a gudanar a Durban ta kasar Afrika ta Kudu. (BAGWAI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China