Sharhi
• Takardun da ake samarwa da iccen gora a garin Jiajiang
Assalam alaikum! Masu sauraro, a yankin makwararin kogin Qingyi dake kudu maso yammacin birnin Chengdu na lardin Sichuan, akwai wani kyakkyawan gari mai tsawon tarihi, wanda ake kiransa Jiajiang. Mazauna garin sun mayar da sana'ar samar da takardu a matsayin ginshikin zaman rayuwarsu zuriya bayan zuriya, har ma an lakabawa garin sunan "garin samar da takardun zane-zane na kasar Sin". Takardun da ake samarwa ta hanyar sarrafa iccen gora, da takardun Xuan da muka gabatar a shirinmu na baya, dukkansu takardu ne da masu zane-zanen gargajiya na kasar Sin suka fi son amfani da su. To, a cikin shirinmu na yau, bari mu je garin Jiajiang dake lardin Sichuan, mu ganewa idanunmu yadda irin wannan takarda take.
• Takardar Dongba da ke da al'adun gargajiya
Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa cikin shirye-shiryenmu na "Asalin Takardun kasar Sin", a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da bayani game da takardar Dongba.

Masu sauraro, a yankunan da ke iyakokin lardunan Yunan, Sichuan da jihar Tibet da ke kudu maso yammacin kasar Sin, akwai wata kabila mai suna Naxi da ke da yawan al'umma dubu 300 kawai, kuma suna da wata fasahar yin takarda ta musamman, kuma an gada wannan fasaha tun shekaru aru-aru da suka wuce, a cikin shekaru fiye da dubu da suka gabata, yayin da 'yan kabilar Naxi ke yin addu'a, su kan yin amfani da wannan takarda don rubuta littattafan addini, sabo da haka, aka lakaba wa wannan takarda suna "takardar Dongba".

• Ana jin kamshin gora daga takardar Yuanshu
Assalamu alaikum, jama'a masu karatu, muna muku lale marhabin a cikin shirin musamman na yau na "Asalin takardu a kasar Sin". Ni ce Salamatu Sabo. A cikin shirinmu na yau, za mu ci gaba da gabatar muku da wani bayani mai lakabi: "Ana jin kamshin gora daga wata takardar Yuanshu".

Jama'a masu karatu, birnin Fuyang na lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin yana dab da kogin Fuchun. Jama'ar wurin sun fi son shuka itatuwan gora sakamakon isashen ruwan sama da a kan yi a wurin. Lokacin da ake tafiya kan hanyoyin dake kan duwatsu, aka wuce gororin da aka shuka. Sabo da haka, ake kiran birnin Fuyang gari na yin takardu. A cikin shirinmu na yau za mu bayyana muku yadda ake yin takardun Yuanshu a wannan wuri.

• Takardar Lian-shi-zhi

Gundumar Yanshan, wata karamar gunduma ce a lardin Jiangxi, amma ta taka muhimmiyar rawa a tarihin kasar Sin na sarrafa takarda. A zamanin da, a nan kasar Sin, littattafai da yawa an wallafa su ne ta hanyar amfani da irin wannan takarda.

Zhang Shikang, wanda ya yi bayeyeniyar fasahar sarrafa takardar Lian-shi-zhi daga zuriya zuwa wata ya fara koyon fasahar sarrafa takardar daga wajen mahaifinsa a lokacin da yake karami. Kakani-kakaninsa sun kaddamar da aikin sarrafa takardar Lian-shi-zhi tun can da.

• Shiga Fang-ma-tan don binciken asalin takarda
A watan Maris na shekarar 1986, cikin kungurmin daji da ke dab da birnin Tian'shui na lardin Gansu da ke arewa maso yammacin kasar Sin, an shafe kwanaki da dama ana ambaliyar ruwa, lamarin da ya haddasa zabtarewar kasa. Ruwa da laka sun kwarara zuwa gindin dutse, inda gidajen ma'aikata masu sare itatuwa suke. Bayan da ruwa ya yi sauki, ma'aikatan sun fara tsabtace filayen da ke kewayen gidajensu, Abin alajabi, suna cikin aikin, sai suka gano wata takarda wadda aka samar da ita shekaru dubu 2 da suka wuce a cikin laka. Takardar da aka lakaba mata suna 'takardar Fang-ma-tan', wato sunan wurin da aka gano ta ke nan, takardar da ta kasance mafi shekaru cikin tsoffin takardun da aka taba ganowa a duniya.
• Takardar Baqiao mai dadadden tarihi
A zamanin yanzu, kayayyakin lantarki na ta kara samun karbuwa a duniya, duk da haka, takardu suna ci gaba da zama kayan rubutu ga akasarinmu, har ma ana daukarta a matsayin daya daga cikin manyan kirkire-kirkire hudu a zamanin gargajiyar kasar Sin, wato baya ga compass, wato na'urar da ke nuna alkibla, da albarushi da kuma dab'i. Sakamakon wannan muhimmiyar kirkira, Bil Adam sun samu damar kara bunkasa al'adunsu. To, a shirinmu na yau, za mu kawo muku labarin takardar Baqiao, takardar da ta fi dadadden tarihi a nan kasar Sin.
More>>
Hotuna
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China