• Bayani kan yadda ake tsugunar da makiyaya a waje guda da kuma bunkasa harkokin ba da ilimi a jihar Xinjiang ta kasar Sin
Sanusi: A bara, gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta shirya wani babban taro game da batun bunkasa jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta. To, yanzu a wane irin halin da al'ummomin jihar suke ciki? Kuma wane irin ci gaba aka samu a jihar a fannoni daban daban? Yau, na gayyaci abokin aikina malam Ibrahim Yaya wanda ya taba kai ziyara a jihar Xinjiang a bara don mu tattauna wadannan batutuwa, musamman batun yadda makiyaya na jihar suka samu wurin kwana, da batun bunkasa harkokin ba da ilmi a jihar. To, malam Ibrahin Yaya, da farko dai, ko za ka iya bayyana wa masu sauraronmu kadan daga cikin abubuwan dake da muhimmanci a jihar Xinjiang?
Sharhi
• Manoman jihar Xinjiang suna jin dadin zaman rayuwarsu ta hanyar raya ayyujan gona bisa ilmin kimiyya

Y: Kande, na samu labarin cewa, 90% na fadin yankin Kizilsu na kabilar Kirgiz na jihar Xinjiang duwatsu da kuma hamada ne. Idan aka ambaci hamada da duwatsu, a kan yi tsammani cewa, tabbas ne wannan wuri na fama da talauci sosai. Ko 'yan kabilar Kirgiz suna fuskantar da wadannan matsaloli?

K: Da ma na kan nuna musu damuwa kamar yadda kake zato. Amma bayan da na ga hotuna da wakilanmu wadanda suka ziyarci yanki a kwanan baya suka dauka kan yankin Kizilsu, na yi mamaki sosai, yankin na da yawan gonaki masu albarka, manoma wurin kuma suna jin dadin zaman rayuwarsu sosai.

Y: Me ya sa haka? Da ma an ji an ce, 'yan kabilar Kirgiz sun yi zamansu kamar mu Hausawa mu kan yi, wato su kan dogara bisa aikin kiwon dabbobi wajen zamansu. Yanzu sun fara aikin gona a maimakon kiwon dabbobi?

Labarai da dumi duminsu
• Bayani kan wata 'yar kabilar Uyghur da wani dan kabilar Kirgiz a jihar Xinjiang
• Bayani kan yadda ake tsugunar da makiyaya a waje guda da kuma bunkasa harkokin ba da ilimi a jihar Xinjiang ta kasar Sin
• Manoman jihar Xinjiang suna jin dadin zaman rayuwarsu ta hanyar raya ayyujan gona bisa ilmin kimiyya
More>>
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China