Jama'a masu karatu, yanzu ga wata muhimmiyar sanarwa. Bana shekara ce ta cika shekaru 70 da kafa gidan rediyon CRI. Shirye-shirye ta gajeren zango na farko da gidan rediyon CRI ya fara watsawa shi ne a shekarar 1941 daga wani kago a wani wuri mai suna Yan'an dake arewa maso yammacin kasar Sin, amma yanzu, yana amfani da harsuna 61 wajen watsa labaru da shirye-shirye iri daban daban ga duniya baki daya, ba ma kawai ta gajeren zango ba, har ma ta zangon FM, kana ana iya karanta da kuma sauraran shirye-shiryenmu a shafuffukan intanet.

A cikin shekaru 70 da suka gabata, akwai tatsuniyoyi masu tarin yawa da suke burge mu. Ma'aikata daga sassa daban daban dake aiki a gidan rediyon CRI suna amfani da harsuna iri daban daban domin gaya wa masu sauraronmu daga sassa daban daban na duniya yadda kasar Sin ke samun ci gaba. Sannan wakilanmu masu tarin yawa wadanda suke aiki a wurare daban daban a duniya suna aiko mana labaru da bayanai kan yadda duniyarmu take samun sauye-sauye. Bugu da kari, masu sauraronmu masu dimbin yawa wadanda ba mu taba ganawa da su ko sau daya a zahiri ba sun zama aminanmu……

Jama'a masu sauraro, mun gode muku kwarai da gaske sabo da kasancewa da gidan rediyon CRI a kowace rana a cikin shekaru 70 da suka gabata. Sabo da haka, tun daga ran 13 zuwa ran 16 ga wata, za mu fara wata gasar kacici kacici mai taken "Muryar dake bayyana tarihin CRI" ta rediyonmu da shafinmu na intanet: https://hausa.cri.cn.

1
• Labarin masu sauraron gidan rediyon CRI
• Daga zangon daga kago na garin Yan'an zuwa tasoshin rediyon FM a biranen da kuke zaune
• CRI na rubuta bayanai kan bunkasuwar kasar da sauyewar duniya bisa sanin ya kamata
•  Muna son muryarka CRI (3)
More>>
Idan kuna son nuna mana "CRI a zukatunku" da fatan alheri na cika shekaru 70 da kafuwar CRI ko kuna fatan kara ci gaban CRI a nan gaba ta hanyar zanen hoto ko da kayan fasahar aikin hannu, sai ku dauki hotunansu, ku aiko mana ta Email, ko kuna iya aiko mana sako tare da hotuna ta gidan waya.

E-Mail: hausa@cri.com.cn

Adireshin Gidan Rediyon Kasar Sin:

Hausa Service CRI-24

China Radio International

P.O.Box 4216 Beijing

P.R.China 100040

© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China