Labarai da dumi duminsu
• Zaben fitattun kungiyoyin masu sauraro goma na CRI
Shekara ta 2011 ta cika shekaru 70 da aka kafa gidan rediyon kasar Sin wato CRI, haka kuma ta cika shekaru 50 da kafuwar kungiyar masu sauraron CRI ta farko a kasashen ketare wato kungiyar masu sauraron gidan rediyon Beijing a kasar Japan. Don tunawa da wannan gaggarumin biki da kuma kara ingiza yalwatuwar kungiyoyin masu sauraron CRI a kasashen ketare, CRI ya fara aikin zaben fitattun kungiyoyin masu sauraro goma a kasa da kasa daga ran 1 ga watan Yuni zuwa ran 1 ga watan Disamba na shekara ta 2011. Za a watsa labaran da suka shafi aikin da harsuna 61 ta hanyoyi daban daban, misali, watsa labarai ta rediyo ko yanar gizo da hotuna da rubutun bayanai da murya da bidiyo da sauransu. CRI zai kafa wata kungiya ta musamman domin gudanar da wannan aikin zabe.
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China