in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamata ya yi a kara kare abubuwan tarihi na al'adun da ake gada daga kakannin kakanni
2010-10-25 20:27:28 cri

Ran 25 ga wata, Mr. Wang Wenzhang mataimakin ministan harkokin al'adun kasar Sin ya nuna cewa, abubuwan tarihi na al'adun da ake gada daga kakannin kakanni su ne albarka'tun al'adun da bil Adam suka kera tare, ban da kokarin da wata kasa ke yi da kanta, ya kamata kasashen duniya su kara yin hadin gwiwa da yin mu'amala da juna.

Mr. Wang Wenzhang ya yi wannan bayani ne a taron dandalin kiyaye abubuwan tarihi na al'adun da ake gada daga kakannin kakanni. Yana ganin cewa, ban da hadin gwiwar da ke tsakanin gwamnatocin kasashe, ita ma hadin gwiwar da ke tsakanin jama'a tana da muhimmanci sosai.

Bisa bincike na farko da aka yi, yawan abubuwan tarihi na al'adun da ake gada daga kakannin kakanni ya kai dubu 870 daga fannonin adabin jama'a, da kide-kiden gargajiya, da raye-raye, da wasan kwaikwayo, da zane-zane, da wasanni, da fasahohin gargajiya, da aikin likita na zamanin da, da al'adun al'ummomi da dai sauransu. (Musa Guo)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China