A yankin Shijingshan dake nan birnin Beijing, Madam Wang Yan ta nunawa wakilinmu kwan fitila irin na tattalin makamashi da gidanta ke amfani da shi:
"Wannan fitila ce dake yin tsimin makamashi da muke amfani da ita, wadda unguwarmu ta ba mu shekara guda da ta gabata. Yanzu tana aiki yadda ya kamata, kuma tana da haske sosai."
Fitilar dake yin tsimin makamashi da Madam Wang ke amfani da ita a gida, wata irin fitila ce wadda hukumar birnin Beijing tayi kokarin bayyana ta cikin 'yan shekarun da suka gabata. Amma a baya, an gamu da matsaloli yayin da ake kokarin samar da fitilun dake yin tsimin makamashi, saboda suna da tsada ga jama'ar kasar Sin.
Tun farkon shekara ta 2008, hukumar birnin Beijing ta kaddamar da wani aiki na "sayen wata fitilar dake yin tsimin makamashi da Yuan 1" ta hanyar bada kudin samun rangwame. A nasa bangaren, mataimakin darektan kwamitin neman bunkasuwa da yin gyare-gyare na birnin Beijing, Mista Zhang Yanyou ya ce:
"Bisa wannan ma'auni, kowane gida na iya samun fitilu 5 wadanda ke yin tattalin makamashi. Idan akwai karin bukata, ana iya sayensu daga masana'antu."
A hakika, bayyana muhimmancin fitilun dake yin tsimin makamashi, daya ne daga cikin matakan da hukumar birnin Beijing ta dauka a fannonin yin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli. Mataimakin shugaban sashin kula da harkokin yin tattalin albarkatu da kiyaye muhalli na kwamitin neman bunkasuwa da yin gyare-gyare na birnin Beijing, Mista Jia Jianting ya ce, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, aikin kawo sauye-sauye ga tsarin sana'o'i ya bayar da babbar gudummawa ga ayyukan yin tsimin makamashi na birnin Beijing, inda ya ce:
"Bayan da aka fara aiwatar da shirin shekaru 5 a karo na 11 a nan birnin Beijing, ana nuna kwazo wajen kawar da kamfanoni sama da 100, wadanda suke fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da yin amfani da makamashi fiye da kima, lamarin da ya sa yawan gudummawar da aikin kawo sauyi ga tsarin sana'o'i ya baiwa ayyukan yin tsimin makamashi na Beijing ya zarce kashi 80 bisa dari."
Har wa yau kuma, Mista Jia ya ce, babban dalilin da ya sa birnin Beijing ke kan gaba a kasar Sin a fannin yin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli shi ne, yana aiwatar da wani cikakken tsari, inda ya ce:
"Muna mayar da hankali sosai kan inganta aikin yin amfani da makamashi, da sauya hanyar da ake bi wajen raya tattalin arziki. A fannin yin tattalin makamashi kuma, hukumomi, kasuwanni, gami da jama'a dukkansu suna yin kokari."(Murtala)