in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan GDP na kasar Sin ya wuce na kasar Japan
2010-09-09 20:52:07 cri
Garba: Bisa kididdigar da gwamnatin kasar Japan ta bayar kwanan baya, a cikin watanni 3, wato daga watan Afrilu zuwa watan Yuni na bana, yawan GDP na kasar Sin ya wuce na kasar Japan. Wannan ya alamta cewa, kasar Sin ta soma hawa kan matsayi na biyu da kasar Japan ta kasance a kai cikin shekaru 40 da suka gabata a fannin tattalin arziki. Bayan an shiga karni na 21, a shekarar 2006, jimillar GDP ta kasar Sin ta wuce ta kasar Ingila, sannan a shekarar 2007, ta wuce kasar Jamus. Ko da yake jimillar GDP ta kasar Sin ta hau kan matsayi na biyu a duk duniya yanzu, amma ko ana iya cewa kasar Sin ta zama kasa mai arziki? Wannan ya zama wani muhimmin batun da ke jawo hankalin mutane. Game da wannan batu, kwanan baya, wakilin CRI ya yi hira tare da Mr. Liu Guangming, mai ba da shawara kan harkar zuba jari a wani kamfanin hada-hadar kudi.

Sanusi: A gun ganawar, Mr. Liu Guangming ya ba da tabbaci kan ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin tattalin arziki, inda Mr. Liu ya ce, "A ganina, wannan wani sakamako ne mai armashi da ke jawo hankalin jama'a, wannan ya alamta cewa, matsayin da kasar Sin ta dauka a fannin tattalin arziki ya dace da matsayin da kasar Sin ta dauka a fannin siyasa a duniya bayan da aka soma aiwatar da manufofin bude kofa ga kasashen waje da yin gyare-gyare kan tattalin arziki."

Garba: Amma, sabo da yawan mutanen kasar Sin ya kai fiye da biliyan 1 da miliyan dari 3, idan an rarraba jimillar GDP ta kasar Sin ga kowane Basine, matsakaicin GDP zai kai kashi 1 cikin kashi 10 ne kawai bisa na kasar Japan. Mr. Liu Guangming ya ce, har yanzu yawan mutanen kasar Sin da yawan kudin shiga da suke samu bai kai dala daya ba a kowace rana ya kai miliyan 150. Bisa ma'aunin kasa da kasa, dukkansu mutane ne masu fama da talauci. Mr. Liu ya ce, "Ko da yake jimillar GDP ta kasar Sin ta kai matsayi na biyu a duniya, amma matsakaicin GDP bai kai matsayi na dari 1 ba, irin wannan bambanci kan sheda cewa, a hakika dai, kasar Sin ba kasa ce mai arziki ba a fannin tattalin arziki."

Sanusi: A hakika dai, jimillar GDP wani adadi ne kawai. Idan kasar Sin da jama'arta suna son zama masu arziki, dole ne kasar Sin ta ci gaba da yin kokari. Alal misali, matsakaicin yawan GDP na kasar Japan ya kai dalar Amurka dubu 37.8 a shekarar 2009, amma irin wannan adadi bai fi dalar Amurka dubu 3 da dari 6 ba a kasar Sin. Mr. Liu Guangming ya kara da cewa, "Hanyar kidaya yawan GDP ba ta daidaita ba sosai, kuma ba ta bayyana bambancin da ke akwai a fannin tattalin arziki ba, kana ba ta bayyana ko ana jin dadin zaman rayuwa, ko a'a ba da dai makamatan haka."

Garba: Bisa tsarin cinikayyar da ake yi, har yanzu, kasar Sin tana karshen layin samar da kayayyakin masana'antu. A cikin kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa, galibinsu suna bata makamashin halittu da 'yan kwadago sosai, amma yawan kayayyaki na fasahohin zamani da kasar Sin ke fitarwa ya yi kadan. Mr. Liu Guangming ya nuna cewa, "Har yanzu, kasar Sin za ta iya ci gaba da bunkasa tattalin arzikinta cikin sauri, amma idan an mai da hankali kan yawan GDP kawai, ba a mai da hankali kan abubuwan da ke kasancewa a bayan GDP ba, wato kasar Sin tana bunkasa tattalin arzikinta bisa yawan jarin da take zubawa kan harkokin yau dakullum da cinikin waje kawai. Amma yawan kudin shiga da jama'a ke samu bai samu karuwa cikin sauri ba. Irin wannan hanya ba za ta iya ba da taimako ga kokarin kara wa jama'a kudin shiga ba, kuma ba za ta iya kara ba da taimako ga kokarin kyautata ingancin zaman rayuwar jama'a ba."

Sanusi: Bugu da kari, idan an yi nazari kan tsarin ilmi da na kiwon lafiya da na ba da tabbacin zaman rayuwar jama'a, za a gane cewa, kasar Sin tana bukatar kyautata da kuma bunkasa tsare-tsare da ayyuka na jin dadin jama'a. Kawo yanzu, yawan kudin da aka kebe wa aikin tarbiyya ya kasa iya biyan bukatar da ake da ita, kuma ana fuskantar matsaloli iri iri wajen ba da tabbacin zaman rayuwar jama'a. Haka kuma, a shekarar 2008 kawai, yawan mutanen da suka rasa aikin yi ya kai miliyan 8 da dubu 860 a garuruwa da birane, kuma yawan tsofaffin da shekarunsu na haihuwa ya wuce 65 ya kai fiye da kashi 12.5 cikin kashi dari, wato ko da yake kasar Sin ba kasa ce mai arziki ba, amma wata kasa ce dake da tsofaffi masu yawan gaske.

Garba: Jama'a masu karatu, wannan ne hakikanin yanayin da kasar Sin ke ciki. Idan tana son zama wata kasa mai arziki, dole ne ta kara yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arziki da canja hanyar bunkasa shi, kuma dole ne ta kara mai da hankali kan yadda za a iya kara yawan kudin shiga da jama'a ke samu da batutuwan ilmi, kiwon lafiya da dai makamatansu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China