in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kasuwa suna kokarin samun kudi a yayin bikin EXPO na Shanghai
2010-06-10 15:21:39 cri
Ibrahim: Bayan da aka bude kofar farfajiyar bikin EXPO na shekarar 2010 da ake yi a birnin Shanghai a ran 1 ga watan Mayu, 'yan kasuwa na gida da na waje suna ta kokarin samun kudi ta hanyoyi daban daban. A cikin shirinmu na yau, za mu duba wannan batu.

Sanusi: E, kamar a wani kantin da ke dakin nune-nunen kayayyakin Madrid na kasar Spaniya, akwai wani babban hoton Ronaldo Luiz, mutumin da ya yi suna kwarai a fannin wasan kwallon kafa a duniya, kuma yanzu haka yake wasan kwallon kafa a kulob din na Real Madrid na kasar Spaniya. Wannan hoto ne ke jawo hankalin dimbin masu yawon bude ido suke ziyartar dakin kasar Spaniya. Mutumin da ke kula da dakin kasar Spaniya ya gaya wa wakilinmu cewa, "Idan ka je babban filin wasan kwallon kafa na kulob din na Real Madrid da ke kasar Spaniya, suna kuma yin hakan, wato za ka iya daukar hoto da a jikin hoton mashahurin dan wasan kwallon kafa. An samu izinin yin hakan."

Ibrahim: A dalilin mashahurin dan wasan kwallon kafan, masu yawon bude ido da yawa sun shiga dakin Madrid na kasar Spaniya. Sabo da haka, wadanda suke aiki a cikin dakin sun yi amfani da wannan dama, inda suka bayyana wa masu yawon bude ido irin abubuwan tarihi da ake sayarwa. "Tufafin yara da kayayyakin ado da jakunkuna, masu zane-zane na Madrid ne suka zana su, kuma za su kafa kantuna a kasar Sin. Yanzu an riga an kafa wani ofis a kasar Sin domin Sinawa su san da wannan tambarin."

Sanusi: A cikin kwanaki 184 da ake tallen bikin EXPO na Shanghai, miliyoyin masu yawon bude ido za su kai ziyara ga bikin, kuma yawan Sinawa masu yawon bude ido zai kai kashi 90 cikin kashi dari. Sabo da haka, bukatar Sinawa su san kayayyakin, wani muhimmin buri ne da 'yan kasuwa suke son cimmawa a yayin bikin.

Ibrahim: A cikin sashen harkokin kasuwanci na dakin kasar Australiya, ana sayar da abubuwan kyauta, kamar su baje da rigar T-shirt da kayayyakin da kasar Australiya ita kadai aka san take samarwa, kamar abincin gina jiki da wasu kayayyakin ado har ma da irin na fatan dabbobi. Wata yarinya wadda ke aiki a dakin kasar Australiya ta gaya wa wakilinmu cewa, abin da suka fi mai da hankali shi ne yadda masu sayayya za su iya sanin kasar Australiya. "A hakika dai, ba mu bukatar samun kudin riba a nan ba, ko shakka babu, muna da shirin yin kasuwanci, amma yanzu, muna fatan masu sayayya za su iya sanin hakikanin kasar Australiya kamar yadda ya kamata a wannan daki."

Sanusi: A dakin kasar Australiya, yawancin masu yawon bude ido sun gaya wa wakilinmu cewa, bayan da suka ziyarci wannan daki, suna son kai ziyara a kasar Australiya. Sabo da haka, a ganin 'yan kasar Australiya, wannan ne ya fi muhimmanci.

Ibrahim: Kamfanin yin burodi na Jing'an wani kamfani ne da ke samar da burodi irin na Faransa, kuma an kafa shi a birnin Shanghai yau shekaru 25 da suka gabata. Yanzu yana da kananan dakunan sayar da burodi fiye da 70 a cikin birnin Shanghai. Kamfanin yin burodi na Jing'an yana sayar da burodi a dakin dake cikin farfajiyar bikin EXPO na Shanghai daidai da farashin da sauran rassansa ke sayarwa, wato bai kara farashinsa ba. Lokacin da take ganawa da wakilinmu, madam Xu Yun, wadda ke kula da dakin sayar da burodi a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai, ta ce, hukumar shirya bikin ta zabi kamfanin yin burodi na Jing'an da ya kafa dakin sayar da burodi, wannan ya tabbatar da cewa, an amince da ingancin burodin kamfanin, kuma wata muhimmiyar dama ce ga kamfanin wajen yada sunansa ga jama'a. "A da, na yi aiki a wani daki daban. Bayan kaddamar da bikin EXPO na Shanghai, ana bukatar mutane a wannan daki, sakamakon haka, na koma wannan daki. A cikin wannan dakin namu, yawan cinikin da muke samu a kowace rana ya kai kusan kudin Sin yuan dubu 10."

Sanusi: Kamfanin Coca-Cola da ya yi suna sosai a duniya ba ya bukatar kara yada sunansa. Amma, wannan kamfani ya kafa wani daki na musamman mai suna "Dakin Jin Dadin Yin Aiki" a farfajiyar bikin EXPO na Shanghai. Mr. David Brooks, babban jami'in tafiyar da harkokin kamfanin Coca-Cola a kasar Sin ya bayyana cewa, "Ana nuna abubuwa iri iri a cikin wani kyallen da aka kafa shi a gaban dakinmu. Jama'a masu yawon bude ido da suke kai ziyara farfajiyar bikin EXPO na Shanghai za su iya ziyarar dakinmu na jin dadin yin aiki, inda za a iya yin lemon kwalba Coca-Cola nan take domin sanin yadda ake yin lemon kwalba Coca-Cola a kamfani." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China