in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kokarin raya yankin Pudong na Shanghai
2010-05-17 17:55:06 cri
Ibrahim: A ran 18 ga watan Afrilu na shekarar 1990, gwamnatin kasar Sin ta sanar da bude kofar yankin Pudong da ke birnin Shanghai ga kasashen duniya domin kara saurin yin gyare-gyare da bude kofar kasar gare su. Ya zuwa yanzu, dimbin gonaki da tafkuna da ke yankin gabashin gabar kogin Huangpu, wato yankin Pudong a Sinance sun riga sun zama yankunan birni na zamani, har ma yanzu yankin Pudong ya riga ya zama muhimmin karfin da ke kara saurin bunkasa tattalin arzikin birnin Shanghai, kuma ya zama alamar da ke nuna yadda kasar Sin ke yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen duniya.

Sanusi: Sabon yankin Pudong yana gabashin birnin Shanghai. Fadinsa ya kai murabba'in kilomita dubu 1 da 210 tare da mazauna miliyan 4 da dubu 120. Yawan GDP na yankin Pudong bai wuce kudin Sin yuan biliyan 6 ba a shekarar 1990, amma wannan adadi ya kai kudin Sin yuan biliyan 400 a shekarar 2009.

Ibrahim: Ana iya ganin muhimman sauye-sauyen da aka samu a yankin Pudong cikin shekaru 20 da suka gabata a shiyyar bunkasa harkokin tattalin arziki da cinikayya ta Lujiazui da ke yankin. Wannan ce shiyyar bunkasa harkokin tattalin arziki da cinikayya ta farko da aka kafa a kasar Sin. Lokacin da yake tabo magana kan irin wadannan sauye-sauye, Mr. Yang Xiaoming, babban direktan kamfanin Lujiazui ya ce, shi ma ya yi mamaki sosai ga irin wadannan sauye-sauye, inda Yang Xiaoming ya ce, "A farkon lokacin soma raya yankin Pudong, babu kome a wurin da ke kusa da ofishin kula da ayyukan raya yankin Pudong, har ma ba a samu wannan ofis cikin sauki ba. Sabo da haka, mun kafa alamun talla guda biyu musamman a kan hanya domin nuna wa jama'a yadda za su iya isa ofishinmu'. A wancan lokaci, idan ka wuce titin Dongfang, yankunan karkara ne kawai, kana iya ganin gonaki da yawa. "

Sanusi: Amma yanzu, an riga an yi manyan gine-gine masu dimbin yawa a shiyyar raya harkokin tattalin arziki da cinikayya ta Lujiazui, har ma daruruwan hukumomin kudi sun riga sun kafa sassansu a shiyyar, kamar su cibiyar harkokin tattalin arziki ta Shanghai, wato "Shanghai World Financial Center" da tsayinta ya kai mita 492 da babban ginin Jin Mao, wato "Jin Mao Tower" da tsayinsa ya kai mita 420.

Ibrahim: A cikin shekaru 20 da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta tsara dimbin manufofin da suke da nasaba da fannoni iri iri ga yankin Pudong kadai. Sakamakon haka, an samu damar gwada hanyoyi iri daban daban wajen kafa wani sabon birni a yankin Pudong. A waje daya, an yi kokarin kafa wata karamar gwamnati a yankin. Mr. Xu Lin, sakataren reshen jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da ke yankin Pudong ya bayyana cewa, "Tabbas ne za a yi kokarin mai da dan Adam a matsayi mafi muhimmanci da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a a yankinmu. Lokacin da ake yunkurin raya tattalin arziki, za a yi kokarin kara neman ci gaban zaman al'umma da kyautata zaman rayuwar jama'a. Bugu da kari, za a yi kokarin kiyaye yanayi mai daukar sauti da ingancin muhalli domin raya tattalin arziki da babu sinadarin Carbon sosai, kuma ba tare da wata tangarda ba a yankin Pudong."

Sanusi: Shiyyar raya fasahohin zamani ta Zhangjiang da aka kafa a watan Yuli na shekarar 1992 na daya daga cikin muhimman shiyyoyin raya masana'antun zamani a yankin Pudong, inda ake da manyan masana'antu da yawa. A shekarar 2009, yawan kudin cinikayya da aka samu a wannan shiyya ya kai fiye da kudin Sin yuan biliyan 100. Amma a ganin Peng Li, mataimakin babban direktan kamfanin gudanar da shiyyar raya fasahohin zamani ta Zhangjiang, gudummawar da wannan shiyya take bayarwa ga zaman al'umma ta fi irin ta tattalin arziki muhimmanci. Mr. Peng Li ya ce, "Ina ganin cewa, ba kawai muna samun moriya a fannin tattalin arziki ba, gudummawar da muka tanadar ga yanayin zaman al'umma da kokarin kyautata tsarin sana'o'in kasarmu ta fi muhimmanci."

Ibrahim: Jama'a masu sauraro, yanzu batun "raya tattalin arziki da babu sinadarin Carbon sosai" tunani ne da yake samun karbuwa a duk duniya, kuma yana yin tasiri kan manufofin raya tattalin arzikin yankin Pudong na Shanghai. Mr. Liu Jiaping, shugaban kamfanin gudanar da shiyyar raya masana'antun samar da manyan injuna ta Lin'gang da ke yankin Pudong yana ganin cewa, "Dole ne mu ba da hidima ga kokarin raya tattalin arziki da babu sinadarin Carbon sosai, kuma za mu samar da injunan da ba za su fitar da sinadarin Carbon sosai ba, alal misali, injunan da suke iya mayar da makamashin kwal ya zama sabon makamashi, da injuna masu aiki da makamashin iska, da injuna masu aiki da makamashin nukiliya da dai sauransu." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China