in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kacici-kacici na EXPO
2010-05-07 22:02:05 cri

Bayanin da ya kamata a karanta kafin a amsa tambayoyi:

"Hai Bao" zata jagorance ku wajen yin ziyara a farfajiyar bukin EXPO na Shanghai

"Hai Bao" za ta jagorance ku wajen yin ziyara a rumfar kasar Sin ta bikin baje koli na kasa da kasa a Shanghai

"Hai Bao" za ta jagorance ku wajen yin ziyara a birnin Shanghai

"Hai Bao" za ta gaya muku labaru game da bikin baje koli na EXPO

"Hai Bao" zata jagorance ku wajen yin ziyara a babban dakin nune-nune na hadin-gwiwar kasashen Afirka a yayin bikin EXPO

Bayan dubun gaisuwa mai tarin yawa tare da fatan alheri da kuma fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing, babban birnin kasar Sin.

Bayan haka muna sanar da ku cewa, daga ran 20 ga watan Fabrairu na bana, mun soma wata gasar kacici-kacici, dangane da 'Bikin baje kolin duniya na birnin Shanghai na kasar Sin'. Kuma za mu kawo karshen gasar a ran 1 ga watan Agusta na wannan shekara. Kamar yadda muka yi muku alkawari, za mu ba da kyaututtuka ga wadanda suka amsa tambayoyin da muka yi daidai.

Ban da wannan kuma, wani abin da zai burge ku shi ne, duk wadanda suka sami lambar yabo ta musmaman cikin wannan gasa za su samu damar kawo ziyarar gani da ido a kasar Sin. Da zuciya daya ne muke fatan ku samu maki mai gamsarwa a cikin wannan gasa.

Ga tambayoyinmu:

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China