Allah ya yi wa shugaban kasar Najeriya Alhaji Umaru Yar'Adua rasuwa a jiya Laraba a birnin Abuja bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya.
Marigayi Yar'Adua ya fito ne daga jam'iyyar PDP inda a karkashin jam'iyyar ce ya samu nasarar zama shugaban kasar Najeriya a shekara ta 2007 kuma ya kasance shugaba na farko dake da ilimin digiri a kasar.
An haifi marigayin ne a cikin zuriyar dake da asali ta fuskar siyasa a Arewacin jihar Katsina a shekara ta 1951.
Haka zalika mahaifin marigayin ya taba zama minista a lokacin gwamnatin farko bayan samun yancin kan Najeriya daga turawan mulkin mallaka a shekara ta 1960 kuma a wanccen lokaci dan'uwansa ya kasasnce shi ne na biyu a kasar a lokacin da Olusegun Obasanjo ya ke rike da mukamin shugaban mulkin soji a kasar a shekara ta 1970.
Marigayi Yar'Adua ya taba zama malamin chemistry wato sanin halittu da dabarun hada magunguna kuma ya taka rawa sosai a bangaren kasuwanci daga bisani sai shiga harkokin siyasa dumu dumu a cikin shekara ta 1980.
Haka kuma ya dan yi fice a cikin kasar kafin tsohon shugaban kasar Obasanjo ya tsaida shi a matsayin dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar PD.P. a karshen shekara ta 2006, ....