in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin kasar Sin ta dauki jerin matakan fama da yunkurin zuba jari a kasuwar cinikin gidaje domin neman karin riba
2010-05-03 16:18:55 cri
Garba: A kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta dauki jerin kwararan matakan fama da yunkurin zuba jari da aka yi a kasuwar cinikin gidaje domin neman karin riba ga tayin da ya dace. A watan Maris na bana, saurin hauhawar farashin gidaje ya kai 11.7% a manya da matsakaitan birane 70 bisa na makamancin lokaci na bara, wato ya kai matsayin koli da ake da shi a tarihi. Mr. Gu Yunchang, mataimakin shugaban kungiyar nazarin sana'ar samar da gidajen kwana ta kasar Sin ya bayyana cewa, hauhawar farashin gidaje ta yi sauri fiye da kima, kuma yunkurin zuba jari domin neman riba ga tayin da ya dace shi ne wani muhimmin dalilin da ya sa hakan. Mr. Gu ya bayyana cewa, "Bayan an shiga karshen kwanaki 10 na watan Maris, farashin gidaje da farashin filaye dukkansu sun hau cikin sauri fiye da kima. Dalilin da ya sa hakan shi ne wasu mutane sun sayi ko sayar da gidaje bisa tayin da ya dace domin neman karin riba. A wasu birane, yawan gidajen da aka saya ko sayar bisa tayin da ya dace domin neman karin riba ya kai kashi 30 zuwa kashi 40 cikin dari bisa jimillar gidajen da aka saya ko sayar."

Sanusi: Mr. Gu yana ganin cewa, yanzu yadda za a iya kayyade batun zuba jari ga tayin da ya dace domin neman karin riba da kayyade saurin karuwar farashin gidaje fiye da kima a kasar Sin, ba ma kawai batu ne na tattalin arziki ba, har ma ya kasance batu ne da ke da nasaba da zaman rayuwar jama'a. Yanzu jama'a suna fuskantar matsaloli da yawa a kokarin sayen gidajen kwana da suke bukata a kasuwa sakamakon hauhawar farashin gidaje. Haka kuma idan farashin gidaje ya hau fiye da kima, hakan na iya haddasa rikicin hada-hadar kudi. Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakai daban daban domin kokarin daidaita wannan al'amari. Mr. Gu ya ce, "A kan dauki matakan kara yawan kudin ruwa da yawan kudin da ake biya a karo na farko lokacin da ake son sayen wani gida domin kawo daidaito a kasuwar cinikin gidaje. Bayan da aka kara yawan kudin da ake biya a karo na farko a lokacin da ake son sayen wani gida, tabbas ne za a kayyade karfin da mutum ke da shi na sayen gida. Haka kuma bayan da aka kara yawan kudin ruwa da ake biya, tabbas ne za a kara jimillar kudin sayen wani gida."

Garba: Matakin musamman na daidaita kasuwar cinikin gidaje da aka dauka a wannan karo shi ne wani mataki ne dake da nufin ganin kasuwannin cinikin gidaje da ake zuba jari domin neman karin riba ga tayin da ya dace kai tsaye, kamar dai misali a biranen Beijing da Shanghai da Guangzhou da Shenzhen da lardin Hainan, inda farashin gidaje ya hau cikin sauri fiye da kima. Mr. Hu Jinghui wanda ke aiki a wani kamfanin cinikin gidaje ya bayyana cewa, "A cikin 'yan shekarun da suka gabata, farashin gidaje ya hau cikin sauri fiye da kima a manyan birane, kamar su Beijing da Shanghai da Guangzhou da Shenzhen. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, ba mazauna wadannan birane ba ne suke sayen gidaje, wasu 'yan kasuwa ne ke zuba jari a kasuwannin gida na wadannan birane domin neman karin riba ga tayin da ya dace. Sakamakon haka, farashin gidaje na irin wadannan manyan birane ya hau cikin sauri fiye da kima, kuma mazauna wadannan birane ba su da isassun kudi domin sayen gidajen da suke bukata."

Sanusi: E, yanzu, wadannan matakan daidaita kasuwar cinikin gidaje sun soma aiki. A nan birnin Beijing, farashin gidaje ya soma raguwa. Kuma a birnin Shenzhen, wani dan kasuwa ya sayar da gidaje daruruwa a karo daya. Mr. Li, wani dan kasuwa daga birnin Wenzhou ya zuba jari kan gidaje fiye da 10 a birnin Shanghai. A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, ya rage farashin gidajensa, kuma ya sayar da su duka. Mr. Li ya ce, "Na taba son sayar da kowane gida kan kudin Sin yuan miliyan 2 da dubu dari 5, amma yanzu, na sayar da kowanensu kan kudin Sin yuan miliyan 2 da dubu dari 2 kawai. Dukkanmu mun nuna damuwar ganin raguwar farashinsu."

Garba: A lokacin da take fama da yunkurin zuba jari a kasuwar gidaje domin neman karin riba ga tayin da ya dace, gwamnatin kasar Sin tana kuma kokarin samar da karin gidaje masu rahusa ga jama'a domin rage farashin gidaje. Mr. Gu Yunchang, mataimakin shugaban kungiyar nazarin sana'ar samar da gidajen kwana ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Makasudin daukar matakan daidaita kasuwar cinikin gidaje shi ne, a yi yaki da yunkurin cinikin gidaje domin neman karin riba. Amma za a ci gaba da sa kaimi ga jama'ar da su sayi gidajen da suke bukata, kuma za a yi kokarin samar da isassun gidaje masu arha ga jama'a." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China