in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kwaskwarima kan manufofin yin amfani da jarin waje domin kyautata tsarin tattalin arzikinta
2010-04-26 10:22:56 cri
Abdul'aziz: A kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta bullo da wata sabuwar manufar yin amfani da jarin kasashen waje. A ran 14 ga wata, jami'an hukumomin gwamnatin kasar Sin sun bayyana a nan birnin Beijing, cewar kasar Sin za ta kyautata tsarin masana'antun dake amfani da jarin kasashen waje domin sa kaimi ga kokarin kirkiro sabbin fasahohin kimiyya da neman ci gaba tsakanin shiyya shiyya cikin daidaito. Bugu da kari, kasar Sin za ta yi kokarin kafa wani yanayin zuba jari da ya fi dacewa ga sauran kasashen duniya domin sa kaimi ga 'yan kasuwa na gida da na waje su yi takara a kasuwa cikin zaman daidai wa daida.

Sanusi: E, malam Ibrahim Yaya, gwamnatin kasar Sin tana kokarin kyautata tsarin tattalin arzikinta domin neman ci gaba ba tare da wata tangarda, ko gurbata muhalli ba. A gun wani taron manema labaru da ofishin yada labaru na gwamnatin kasar Sin ya shirya a ran 14 ga wata, Mr. Zhang Xiaoqiang, mataimakin shugaban kwamitin neman ci gaba da yin kwaskwarima na kasar Sin ya bayyana wa manema labaru muhimman abubuwan da ke cikin "wasu ra'ayoyi kan yadda za a iya ci gaba da yin amfani da jarin kasashen waje ta hanyoyin da suka dace" da gwamnatin kasar Sin ta bayar, inda Mr. Zhang ya ce, "A cikin ra'ayoyin da aka bayar, da farko an jaddada cewa za a kyautata tsarin masana'antun dake amfani da jarin kasashen waje, musamman za a sa kaimi ga baki 'yan kasuwa da su zuba jari a masana'antun kere-kere na zamani da masana'antun da ke amfani da sabbin fasahohin zamani da fannonin ba da hidima irin ta zamani da kuma fannonin da ke da nasaba da sabuwar hanyar amfani da makamashi da dai masana'antu marasa gurbata muhalli. A waje daya, ba za a amince da a zuba jari a masana'antu wadanda suke gurbata muhalli da yin amfani da makamashi da yawa da kuma masu cin albarkatun kasa sosai ba. Sannan, ana sa kaimi ga baki 'yan kasuwa da su zuba jari a yankunan tsakiya da na yammacin kasar Sin. Haka kuma, ana fatan za a iya samun karin dabarun yin amfani da jarin kasashen waje da dai sauransu."

Abdul'aziz: Bisa wannan muhimmiyar takardar da gwamnatin kasar Sin ta bayar, za a yi kwaskwarima kan "sana'o'in da za su iya yin amfani da jarin kasashen waje". Wannan ya kasance tamkar wata muhimmiyar takardar gwamnati da ke ba da jagoranci ga baki 'yan kasuwa, bayan da aka bullo da wannan takarda a shekarar 1995, an yi mata gyara har sau 4. Mr. Zhang Xiaoqiang ya kara da cewa, makasudin sake gyara wannan takarda yanzu shi ne biyan bukatun da ake da su wajen sauya salon tattalin arzikin kasar Sin, inda Zhang Xiaoqiang ya ce, "Da farko dai, za a tsaya tsayin daka kan matsayin kara bude kofa ga kasashen waje domin neman ci gaba da kara yin gyare-gyare kan tsarin tattalin arziki. Sannan yanzu ana aiwatar da shirin farfado da muhimman sana'o'i goma, dole ne a sa kaimi ga kokarin yin amfani da sabbin fasahohin zamani da sabbin hanyoyin samar da kayayyaki a cikin sabbin masana'antu. Haka kuma, yanzu kasar Sin tana kokarin farfado da sabbin manyan sana'o'i, sabo da haka, muna fatan baki 'yan kasuwa za su iya zuba jari a masana'antun da ke da nasaba da sabon makamashi da sabbin kayayyaki da na samar da magunguna irin na zamani da dai sauransu."

Sanusi: Ya zuwa karshen shekarar bara, yawan masana'antu da kamfanoni masu jarin kasashen waje da gwamnatin kasar Sin ta amince aka kafa su a kasar ya kai fiye da dubu 680, kuma jimillar jarin kasashen waje da aka zuba kai tsaye a kasar Sin ya kai fiye da dalar Amurka biliyan 945.

Abdul'aziz: Bisa wannan sabuwar takardar da gwamnatin kasar Sin ta bayar, an ce, idan baki 'yan kasuwa wadanda suke zuba jari a yankunan gabashin kasar Sin su zuba jari a yankunan yammacin kasar, gwamnatin kasar Sin za ta samar musu karin tallafi. Amma a waje daya, lokacin da take sa kaimi ga baki 'yan kasuwa da su zuba jari a kasar Sin, gwamnatin kasar Sin tana kuma mai da hankali kan yadda za a kiyaye ikon mallakar ilmi da samar da wani yanayi mai kyau ga baki 'yan kasuwa. A gun taron manema labaru da aka shirya, madam Ma Xiuhong, mataimakiyar ministan kasuwanci na kasar Sin ta bayyana cewa, "Kara karfin kiyaye ikon mallakar ilmi wani muhimmin nauyi ne da ke bisa wuyanmu wajen kyautata yanayin zuba jari a nan gaba. Ina da imani cewa, gwamnatin kasar Sin za ta kara kyautata tsarin kiyaye ikon mallakar ilmi, kamar tsarin dokoki bisa sakamakon da ta riga ta samu yanzu."

Sanusi: Madam Ma Xiuhong ta ce, yanzu kasar Sin tana kara saurin raya masana'antu da mayar da yankunan karkara su zama garuruwa da birane. Kasar Sin tana fatan baki 'yan kasuwa za su iya samun karin ci gaba lokacin da suke halartar taruka da suka shafi raya kasar Sin. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China