in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Geely na kasar Sin ya samu nasarar sayen kamfanin Volvo
2010-04-19 10:48:07 cri
Ibrahim: to, jama'a masu sauraro, barka da dawowarku a shirinmu na yau na Tattalin Arzikin kasar Sin. A ran 28 ga watan Maris na bana, kamfanin kira motoci na Geely na kasar Sin da kamfanin kirar motoci na Ford na kasar Amurka sun rattaba hannu kan yarjejeniyar sayen takardun hannun jari a birnin Goteborg, birni mafi girma na kasar Sweden, inda kamfanin kira motoci na Geely ya kashe dalar Amurka kimanin biliyan 1 da miliyan dari 8 ya sayi dukkan takardun hannun jari na kamfanin kira kananan motoci na Volvo da sauran kadarorin kamfanin. Wannan ne kudi mafi yawa da wani kamfanin kasar Sin ya kashe domin sayen wani kamfanin kira motoci na kasashen waje gaba daya. Sabo da haka, wasu mutane sun yi sharhi cewa, wannan abin al'ajabi ne da kamfanin kasar Sin ya yi kamar "wani maciji ya cinye wata giwa." Amma wasu sun bayyana cewa, samun nasarar sayen kamfanin kira motoci na Volvo daga hannun kamfanin kira motoci na Ford mafari ne kawai. Idan kamfanin Geely da aka kafa shi yau shekaru 14 da suka gabata yana son tafiyar da kamfanin Volvo da aka kafa shi yau shekaru 86 da suka gabata kamar yadda ake fata, kamfanin Geely yana fuskantar kalubale da yawa.

Sanusi: E, haka ne. A lokacin da yake bayyana dalilin da ya sa kamfanin Ford ya zabi kamfanin Geely na kasar Sin, Mr. Lewis Booth, jami'in farko da ke kula da harkokin kudi a kamfanin Ford ya bayyana cewa, "Kamfanin Ford ya sayar da kamfanin Volvo ne domin nema wa Volvo wani sabon uban gida. Ya kamata wannan sabon uban gida yana da tunani iri daya da kamfanin Ford wajen raya harkokin kamfanin Volvo. Yau, na gaya muku cewa, mun samu nasarar samun wannan sabon uban gida, shi ne kamfanin Geely."

Ibrahim: Amma malam Sanusi, ka ga kasar Sin kasa ce mai tasowa. Me ya sa kamfanin Ford ya sayar da kamfanin Volvo wanda ke samar da kananan motoci masu tsada sosai ga wani kamfanin kasar Sin, wanda ke samar da kananan motoci masu arha?

Sanusi: e, malam Ibrahim, wannan tambaya ce mai ma'ana. Amma idan mun yi nazari kan wasu adadi, za mu gane dalilin da ya sa kamfanin Ford ya sayar da kamfanin Volvo ga wani kamfanin kasar Sin. Da farko dai, a cikin 'yan shekarun nan, yawan kananan motoci kirar Volvo da aka sayar da su yana ta raguwa. Amma a shekarar 2009, yawan kananan motoci masu tsada da aka sayar da su a kasar Sin ya karu da fiye da kashi 40 cikin kashi dari. Daga cikinsu, yawan kananan motoci kirar Volvo da aka sayar da su a kasar Sin ya karu da fiye da kashi 80 cikin dari. Daga karshe dai, me ya sa aka zabi kamfanin Geely? Bisa rahoton sha'anin kudi da kamfanin Geely ya gabatar, yawan ribar da kamfanin Geely ya samu a shekarar 2008 ya kai kashi 20 cikin kashi dari bisa na jimillar kudin da ya samu. Ba safai a kan ga irin wannan karfin samun riba ba a duk duniya. Bugu da kari, kamfanin Geely ya dauki alkawarin cewa, ba zai canja matsayin tambarin Volvo da yake dauka a duniya ba, kuma ba zai daidaita tsarin kamfanin Volvo ba, har ma hedkwatar tafiyar da kamfanin Volvo da hedkwatar yin nazari na kamfanin za su ci gaba da aiki a birnin Goteborg, kuma jami'an kamfanin Volvo na yanzu su ne za su ci gaba da tafiyar da kamfanin. Mr. Li Shufu, shugaban kamfanin Geely na kasar Sin ya ce, "Geely shi ne Geely, Volvo shi ne Volvo. Mun sani, Volvo tambari ne da aka kirkiro a kasar Sweden da ke nahiyar Turai ta arewa. Idan ya bar Sweden, to ba Volvo ba ne, zai zama wani tambarin da ba shi da tushe. A kamfanin Geely, ba za a kera kananan motoci kirar Volvo ba, kuma a kamfanin Volvo, ba za a kera kananan motoci kirar Geely ba."

Ibrahim: to, malam Sanusi, idan kamfanin Geely ya yi haka, mene ne kamfanin Geely zai iya samu daga wannan yerjejeniyar sayen kamfanin Volvo?

Sanusi: Mr. Zhao Fuquan, mataimakin shugaban kamfanin Geely ya ba da amsa cewa, kamfanin Geely ya fi mai da hankali kan fasahohin da kamfanin Volvo ke da su. Zhao Quanfu ya ce, "Kamfanin Geely ne ya mallaki dukkan takardun hannun jari na kamfanin Volvo. Sabo da haka, zai samu muhimman fasahohi da ikon mallakar ilmi da kamfanin Volvo ke da shi. Za mu yi koyi daga kamfanin Volvo domin kyautata ingancin kananan motoci kirar Geely, sannan za mu iya samun ci gaba tare."

Ibrahim: Amma, malam Sanusi, kamfanin Geely wani karamin kamfanin kera motoci ne a duniya, yaya zai iya tafiyar da kamfanin Volvo da ya fi shi girma?

Sanusi: E, wannan matsala ce da ake nuna damuwa a kanta. Amma Mr. Li Shufu, shugaban kamfanin Geely ya ce, yana da dabarar daidaita wannan matsala. In ji Li Shufu cewa, "Matsala mafi tsanani da take kasancewa a kamfanin Volvo shi ne yawan motocin da yake samarwa ya yi kadan idan aka kwatanta shi da na kamfanin Marsandi da na kamfanin BMW. Idan yawan motocin da yake samarwa ya karu, matsakaicin kudin kera motoci da za a kashe kan kowace mota zai ragu, sabo da haka, farashin kowace mota zai ragu. Sakamakon haka, za a iya samun riba." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China