in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birnin Wuxi yana mai da hankalin raya sabon salon masana'antu
2010-03-29 09:05:30 cri
Birnin Wuxi da ke gabashin kasar Sin na daya daga cikin biranen da suka shahara a fannin yawon bude ido a kasar Sin. A kan kira shi "lu'ulu'u da ke tafkin Tai" sabo da yana bakin tafkin Taihu. A cikin 'yan shekarun nan, birnin Wuxi yana kokarin raya sana'o'in manhaja da ba da hidima irin na zamani sabo da yana kusa da birnin Shanghai, birni mafi girma a kasar Sin, yana da karfin tattalin arziki da yawan kwararrun da suke zaune a birnin da kuma aiki.

Birnin Wuxi wuri ne da yake kan gaba wajen raya masana'antu a kasar Sin yau shekaru dari 1 da suka gabata. A cikin shekaru 30 da suka gabata, masana'antu na birnin Wuxi sun samu ci gaba cikin sauri sosai, musamman birnin yana da karfi sosai wajen samar da kayayyakin sassaka da injuna da sauran sana'o'in kere-kere. A cikin 'yan shekarun nan, birnin Wuxi ya soma yin kokarin raya sana'o'in da ba sa gurbata muhalli da sabbin sana'o'in zamani domin canja hanyar raya tattalin arziki, kamar su sana'o'in manhaja da ba da hidima irin na zamani. Kamfanin iSoftStone shi ne kamfani mai mallakar fasahar zamani na farko da aka kafa shi a birnin Wuxi. A shekara ta 2007, wannan kamfani ya shiga birnin Wuxi, sannan ya samu ci gaba sosai. Yawan kudin da ya samu domin ba da hidima irin na zamani ya kai fiye da dalar Amurka miliyan 60, wato ya ninka sama da sau guda bisa na shekarar 2008. Lokacin da yake bayyana dalilin da ya sa ya kafa kamfaninsa a birnin Wuxi, Mr. Lin Jian wanda ke ba da taimako ga mataimakin shugaban kamfanin ya ce, "Ko da yake muna da sauran zabe a yankunan da ke kusa da kogin Yangtze, amma dalilin da ya sa muka zabi wannan wuri shi ne, ba ma kawai gwamnatin birnin Wuxi tana da manufofin sa kaimi ga kokarin raya sana'ar ba da hidima irin na zamani ba, har ma ta kan tura ma'aikatanta zuwa kamfaninmu domin neman ra'ayoyinmu, sannan cikin sauri ne ta kan bullo da matakan da suke dacewa domin tallafa mana."

Game da manufofin tallafawa kamfanoni masu mallakar fasahohin zamani da gwamnatin birnin Wuxi ta tsara, Mr. Fang Wei, mataimakin magajin birnin Wuxi ya ce, lokacin da take zabar kamfanoni wadanda suke kan gaba wajen mallakar fasahohin zamani, gwamnatin ta fi mai da hankali kan makomar kayayyakinsu da karfinsu na fitar da kayayyakinsu zuwa ketare. Sabo da haka, ko da yake wasu daga cikinsu kanana ne yanzu, amma idan suna da kyakkyawar makoma, suna kuma samun tallafin kudi daga wajen gwamnatin. Mr. Fang Wei ya ce, "Ba mu iya nuna musu goyon baya bayan da suka samu nasara, kuma su zama manyan kamfanoni ba. A ganinmu, tallafin kudin da muka samar musu jari ne da muke zubawa domin tinkarar hadarurrukan da za su iya tasowa. Idan gwamnatin tana tsammanin cewa, wani kamfani yana da nagartattun ma'aikata da kyakkyawar kasuwa da kyakkyawar makoma da kuma wani kyakkyawan tsarin sayar da kayayyaki, to, za ta iya tallafa mata. Idan wani kamfani ya zama kamfanin da muka zaba, zai iya samun tallafin kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan miliyan 5 zuwa miliyan 10. Ba su bukatar mayar da wadannan kudi ga gwamnati."

Mr. Ni Bin, shugaban hukumar kasuwanci ta birnin Wuxi ya bayyana cewa, sabo da babu isassun zauruka domin gina sabbin masana'antu, birnin Wuxi ya dauki matakan kaurar da wasu masana'antun gargajiya, ko yin kwaskwarima kan tsoffin zaurukan masana'antu domin nuna namijin kokarinsu wajen raya masana'antu masu mallakar fasahohin zamani. Mr. Ni ya ce, "Mun kafa unguwannin raya masana'antu masu mallakar fasahohin zamani da yawansu ya kai 10. A cikin wadannan unguwanni, mun samar da cikakkun ayyukan yau da kullum domin ba da kyakkyawar hidima ga kamfanonin da suka kafa masana'antu a ciki."

Lokacin da gwamnatin birnin Wuxi take mai da hankali kan masana'antu masu mallakar fasahohin zamani, tana kuma mai da hankali wajen shigar da kwararru iri iri. Alal misali, ta bayar da wata manufa da cewa, idan wani kamfani ya dauki wani dalibin da ya gama karatu daga jami'a, to, gwamnatin za ta samar wa wannan kamfani kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan dubu 4 domin ci gaba da horar da wannan dalibi. A waje daya, wannan dalibi yana iya samun kudin tallafi da yawansa ya kai kudin Sin yuan dubu 1. Sannan gwamnatin wurin ta sa kaimi ga kamfanoni da su yi hadin gwiwa tare da jami'o'in wajen horar da kwararrun da suke bukata. Mr. Lin Jian wanda ke ba da taimako ga mataimakin babban direktan kamfanin iSoftStone ya ce, "Lokacin da muke kokarin shigowar masana, muna kuma kokarin horar da kwararrun da muke bukata a nan gaba. Jami'ar Carnegie Mellon ta kasar Amurka da gwamnatin birnin Wuxi da kamfaninmu mun yin hadin gwiwa mun kafa hukumar farko ta horar da kwararrun da za su mallaki fasahar IT. A shekarar 2009, yawan mutanen da suka gama karatu daga jami'o'i, kuma muka dauka ya kai fiye da 1200, galibinsu sun fara yin aiki a kamfaninmu."

Mr. Ni Bin, wato shugaban hukumar kasuwanci ta birnin Wuxi ya ce, bisa gudummawar da masana'antu masu mallakar fasahohin zamani suka bayar, yanzu birnin Wuxi ya soma yin ban kwana da masana'antun gargajiya wajen raya tattalin arziki. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China