in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta dauki jerin matakai domin sa ido kan kasuwar gidaje
2010-03-18 09:09:34 cri
A shekarar 2009, kasuwar cinikin gidaje ta kasar Sin ta shiga mawuyacin hali a cikin gajeren lokaci sakamakon rikicin hada-hadar kudi na duniya, ta samu farfadowa sosai, wato yawan gidajen da aka sayar, da kuma farashinsu dukkansu sun samu karuwa cikin sauri. Sabo da haka, wasu kafofin yada labaru sun ba da sharhi cewa, wai kasuwar cinikin gidaje ta kasar Sin ta haura a shekarar 2009. Har ma wasu kafofin yada labaru sun kwatanta farashin gidajen birnin Beijing da na gidajen da marigayi Michael Jackson na kasar Amurka ya saya, sun ce, "ana iya biyan kudin sayen gidajen Michael Jackson, amma ba za a iya biyan kudin sayen gidajen birnin Beijing ba". Sabo da haka, tun daga karshen shekarar bara, gwamnatin kasar Sin ta dauki jerin matakai domin rage saurin karuwar farashin gidaje a wasu birane da kuma sa ido kan kasuwar cinikin gidaje.

A ganin wasu jama'ar kasar Sin, ba su iya amincewa da farashin gidaje na yanzu ba.

"Bisa albashinmu, ba mu iya biyan kudin sayen gida, har ma dole ne mu nemi rancen kudi domin biyan kudin da dole ne mu biya a mataki na farko."

"A matsayin fararen hula, muna son sayen wani gida, amma idan farashinsu ya yi ta hauhawa kamar haka, da wuya mu iya sayen gida."

Wani rahoton tattalin arziki na cibiyar nazarin kimiyyar zaman al'umma ta kasar Sin ya nuna goyon bayan wadannan ra'ayoyi na jama'a. Wannan rahoto ya nuna cewa, a karshen shekarar 2008, gwamnatin kasar Sin ta dauki jerin matakan raya kasuwar cinikin gidaje domin tinkarar rikicin hada-hadar kudi na duniya. A waje daya, farashin gidaje ya ragu sakamakon raguwar yawan gidajen da aka sayar sosai. Wannan kuma ya sa kasuwar cinikin gidaje ta samu farfadowa. Sakamakon haka, farashin gidaje ya karu cikin sauri, kuma yawan kudin da mutum zai biya domin sayen gida ya karu kwarai, har ma ya fi karfin jama'a. Bugu da kari, sabo da tattalin arzikin kasar Sin ya soma kubuta daga rikicin hada-hadar kudi na duniya. Tun daga karhen shekarar 2009, gwamnatin kasar Sin ta soma soke matakai an alfarma da ta dauka domin raya kasuwar cinikin gidaje. Game da wannan manufar da gwamnatin kasar Sin ke aiwatarwa, shehun malami Dong Fan wanda yake nazarin kasuwar cinikin gidaje a jami'ar horar da malamai ta Beijing ya bayyana cewa, wadannan matakai za su taka rawa wajen rage yawan kudin da ake zubawa a kasuwar cinikin gidaje.

"Tabbas ne matakin kara yawan kudin da dole ne a biya a karo na farko lokacin da ake sayen gida, yana da ma'ana sosai wajen kayyade yunkurin zuba jari a gidaje domin neman karin riba. A kan sayi karin gidaje ne domin neman riba. Sabo da haka, idan wani iyalin da ke da gidan kwana ya kara sayen gidaje, tabbas ne yana son neman riba."

Bisa matakan da gwamnatin tsakiya ta dauka, bankunan kasar Sin sun kuma soma kayyade yawan rancen kudin da suke samar wa masu sayen gidaje. Mr. Li Daokui, shugaban cibiyar nazarin tattalin arzikin kasar Sin da ma na duniya a jami'ar Tsinghua ta kasar Sin ya bayyana cewa, "Irin wadannan matakai suna dacewa da manufofin da gwamnatin tsakiya take aiwatarwa domin fama da yunkurin zuba jari a kasuwar cinikin gidaje ga damar da ta dace domin neman karin riba. Ina tsammani cewa, sauran bankunan kasuwanci ma za su dauki wannan mataki. Sakamakon haka, mai yiyuwa ne yawan gidajen da ake sayarwa da farashinsu su ragu."

Ba ma kawai gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan daidaita kasuwar cinikin gidaje ba, har ma ta dauki matakan sarrafa kasuwar samar da filayen gina gidaje da ayyukan gina gidaje daya bayan daya. Game da irin wadannan matakai, Mr. Yun Xiaosu, mataimakin ministan albarkatun gonaki na kasar Sin ya ce, za a ci gaba da fama da laifin adana filayen gina gidaje. Ya ce, "Ya zuwa karshen shekarar 2009, yawan filayen gina gidaje da suke hannun kamfanonin gina gidaje ya kai kusan hektoci miliyan dari 2 wadanda za su iya isa bukatun gina gidaje da kamfanonin gina gidaje suke da su a cikin shekaru 2 ko 3 masu zuwa. A bana, za mu kara sa ido kan yadda suke amfani da wadannan filaye, kuma za mu neme su da su yi amfani da su bisa ka'idojin da aka tsara a cikin kwangila. Bugu da kari, za mu dauki kwararan matakan fama da laifin cinikin irin wadannan filaye bisa doka." (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China