in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lardin Anhui yana kokarin ba da inshorar kiwon lafiya a yankunan karkara lokacin da yake raya aikin gona
2010-03-11 16:00:25 cri
A watan Janairu na shekarar 2010, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwa ta kasar sun bullo da takarda mai lamba 1, inda aka fi mai da hankali kan batutuwan da suke da nasaba da aikin gona da manoma da yankunan karkara a cikin jerin shekaru 7 da suka gabata. A cikin shirinmu na yau, za mu bayyana muku yadda lardin Anhui da ke tsakiyar kasar Sin yake kyautata tsarin ba da tabbaci ga al'ummomi. Sakamakon haka, zaman rayuwar manoman wannan lardi yana ta samun kyautatuwa sosai.

Lardin Anhui na daya daga cikin muhimman lardunan da ke kan gaba wajen samar da amfanin gona a kasar Sin. A shekarar 2009, an gamu da bala'in fari da ba safai ake ganin irinsa ba a cikin shekaru 50 da suka gabata a lardin, amma yawan amfanin gona da aka samu a lardin a cikin duk shekarar 2009 ya karu da kilogram miliyan 250 bisa na shekarar 2008. Mr. Niu Yunsheng, shugaban hukumar aikin gona ta lardin Anhui ya ce, "Jimillar amfanin gona da aka samu a lardinmu a shekarar 2009 ta kai fiye da kilogram biliyan 30, wato an yi girbin hatsi cikin jerin shekaru 6 da suka gabata, har ma an samu kaiwa wani sabon matsayi a tarihi cikin jerin shekaru 4 da suka gabata."

Niu Yunsheng ya ce, dalilin da ya sa aka samu girbi a shekarar da ake fama da bala'in fari shi ne a cikin jerin shekarun da suka gabata, gwamnatin lardin Anhui ta mai da hankali sosai wajen nazari da kuma yin amfani da sabbin ire-iren hatsi a kokarin samun karin amfanin gona. Bugu da kari, gwamnatocin matakai daban daban sun yi kokarin tallafawa aikin gona domin sa kaimi ga masu sana'ar aikin gona. Mr. Niu ya ce, "Yawan kudin da ake zubawa a fannin aikin gona a lardin Anhui yana ta karuwa. Alal misali, muna tallafawa sabbin ire-iren hatsi da amfanin gona da kayayyakin da ake amfani da su a fannin aikin gona da injuna da nu'urorin aikin gona."

Sakamakon haka, lardin Anhui ya samu karfi sosai wajen raya tattalin arzikin aikin gona. Alal misali, ya yi kokarin raya sana'o'in sarrafa amfanin gona da kayan abinci iri iri. Kamfanin Liangfu na Anhui da ke samar da garin alkama ya kafa wata unguwar sarrafa amfanin gona, inda za a iya samar da karin garin alkama da yawansa ya kai kusan ton dubu dari 5. Mr. Pan Xingzhe, babban direktan kamfanin Liangfu na Anhui ya gaya wa wakilinmu cewa, "Bayan da muka samar da wadannan sabbin ayyuka, yawan kudin da muke samu ya karu da kudin Sin yuan biliyan 1 da miliyan dari 2 a kowace shekara, kuma matsakaicin yawan kudin da kowane iyalin manoma ya samu ya karu da kudin Sin yuan dubu 2 da dari 3 a kowace shekara."

Lokacin da lardin Anhui yake kokarin raya aikin gona da kuma canja hanyar raya shi, ana kuma kokarin ba da tabbaci ga jama'a, musamman ba da inshorar kiwon lafiyar manoma.

A cikin 'yan shekarun nan, Wu Mingde, wanda ya kai fiye da shekaru 60 a duniya, wani manomi ne na birnin Fuyang, ya kan yi juwa. Bayan da likitan da ke aiki a kauyensu ya duba jikinsa, Wu Mingde ya sayi maganin da yawan kudinsa ya kai Yuan kusan 19 ne kawai. Sannan, bisa ka'idojin sabon tsarin ba da inshorar kiwon lafiya a yankunan karkara, gwamnatin wuri ta mayar masa kudin da yawansa ya kai kashi 40 cikin kashi dari bisa jimillar kudin da aka kashe, sabo da haka, daga karshe, yawan kudin da Wu Mingde ya kashe bai fi yuan 11 ba wajen sayen dukkan magungunan da yake bukata.

"Jama'ar da ke zaune a yankunan karkara suna jin dadin wannan sabon tsarin ba da inshorar kiwon lafiya. Wannan sabon tsari yana warware matsalolin da ke kasancewa a gabanmu."

A yankunan karkara na birnin Chaohu na lardin Anhui, yawan masu sana'ar aikin gona da suka shiga wannan tsarin ba da inshorar kiwon lafiya ya riga ya kai fiye da miliyan 3 da dubu dari 5. Ma Daqing wanda yake zaune a wani kauyen gundumar Wuwei ya ce, "A shekarar 2009, dana ya kamu da wani ciwo. Mun kashe kudin Sin yuan dubu 73 domin ganawa da likitoci a asibitin da ke lardin Guangdong. Bayan na dawo garinmu, na gabatar da dukkan rasidin wadannan kudi, sannan ofishin kula da wannan tsarin ba da inshorar kiwon lafiya ya mayar mini kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan dubu 30. Amma ka sani, na biya kudin Sin yuan 20 ne kawai lokacin da na shiga wannan tsari."

Tun daga shekarar 2003 zuwa yanzu, sabo da karuwar kudin da gwamnatin kasar Sin ke zubawa kan wannan tsarin ba da inshorar kiwon lafiya, a cikin 'yan shekarun nan, lardin Anhui ya samu ci gaban wannan tsari. Yanzu, an riga an shimfida wannan tsari a kusan dukkan yankunan lardin Anhui. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China