in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da samun isassun kayayyaki a kasuwa lokacin da Sinawa suke murnar bikinsu mafi muhimmanci
2010-02-19 16:41:42 cri
Yau kwana na biyu ne da Sinawa ke murnar bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta watansu. A cikin shirinmu na yau, za mu kai ku zuwa wasu manyan kantunan da ke birnin Beijing da yankin Alta na jihar Xinjiang da birnin Canton domin sanin yadda Sinawa suke sayen kayayyakin masarufi domin taya murnar sabuwar shekara.

A kusan dukkan manyan kantuna da kasuwannin da ke birnin Beijing, wakilanmu sun ga dimbin mutane suna ribibin sayen kayayyaki iri iri. Alal misali, a wani kantin Carrefour da ke kusa da gidan rediyo CRI, yawan masu sayayya ya karu da kashi 30 zuwa kashi 40 bisa kashi dari. Mr. Wang Zhengjiang, wani manajan wannan babban kanti ya ce, "A cikin 'yan kwanakin da suka gabata, yawan masu sayayya ya karu sosai. Amma sabo da mun riga mun tanadi kayayyaki a cikin kantinmu yau wata daya da ya gabata, har ma mun yi hayar wani daki domin ajiye kayayyakinmu. Sakamakon haka, za mu iya samar da isassun kayayyakin da masu sayayya suke bukata."

Mr. Yang, wanda yake sayen kayayyaki iri iri ya ce, bikin bazara, wato bikin sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, biki ne mafi muhimmanci ga dukkan iyali da danginsa. A yayin da ake murnar wannan biki, za su iya samun lokacin saduwa da junanmu. Mr. Yang ya ce, "Ina sayen kayayyaki domin share fagen murnar sabuwar shekara. Na riga na sayi wasu kayayyakin kawata dakuna, kamar baki 'Fatan Alheri' da wasu furanni. Kuma zan sayi wasu 'ya'yan itatuwa da nama domin murnar wannan sabuwar shekara tare da 'ya'yana."

Bayan da aka shiga shekara ta 2010, an yi dusar kankara mai tsanani da ba a gamu da irinta ba cikin shekaru 60 da suka gabata a yankin Alta da ke jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin. Wannan bala'in ya kawo illa sosai ga zaman rayuwar jama'a da aikinsu. Amma a jajibirin sabuwar shekarar gargajiya ta Sinawa, mazauna yankin Alta suna sayen kayayyakin da suke bukata domin murnar wannan sabuwar shekara kamar yadda suka saba yi a da.

An bayyana cewa, bayan da aka gamu da wannan bala'in dusar kankara a yankin Alta, gwamnatin jihar Xinjiang ta riga ta yi sufurin kayayyakin lambu da sauran abinci iri iri da yawansu ya kai kusan ton 800 zuwa yankin Alta. Mr. Jiao Zhongxun wanda ke rike da wani kanti a birnin Alta ya ce, "Ana samar da isassun kayayyakin da ake bukata, kuma farashinsu ya yi daidai da na bara. Yanzu mutane da yawa sun soma sayen kayayyaki iri iri domin murnar wannan sabuwar shekara."

Kantin "Liangxianglou" yana daya daga cikin kantunan da suka fi shahara a birnin Canton. A wannan kantin "Lianxianglou", ana sayar da kayayyakin tande-tande da lashe lashe. A jajibirin bikin murnar sabuwar shekara ta gargajiya ta Sinawa, yawan mutanen da suke sayen kayayyaki a kantin "Lianxianglou" ya karu sosai. Madam Liang Zhijun, manajar wannan kanti ta ce, "Tun farkon shekarar da muke ciki, mun samar da karin ire-iren kayayyaki domin biyan bukatun da masu sayayya suke da su domin murnar sabuwar shekara. Amma sabo da farashin kayayyaki ya karu, farashin kayayyakin tande-tande da lashe-lashe da muke sayarwa ma ya karu kadan. Wannan bai kawo illa ga yawan kayayyakin da muke sayarwa ba."

Yanzu, ba ma kawai ana sayen kayayyaki a kantuna kai tsaye ba, har ma wasu mutane sun fi son sayen kayayyaki a wasu tasoshin Intanet na sayar da kayayyaki. Madam Huang Jia, wadda ke aiki a wata mashahuriyar tashar Intanet mai suna "Tao Bao" inda ake sayar da kayayyaki, ta ce, a watan Janairu na bana kawai, yawan kudin da aka kashe domin sayen kayayyaki a tasharsu ya kai kudin Sin yuan biliyan 1. Madam Huang ta bayyana cewa, "Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da muka yi, an ce, yawan kudin da aka kashe domin sayen abinci kawai ya kai kimanin kudin Sin yuan miliyan dari 7. Alal misali, wani mutum ya kashe kudin Sin yuan dubu 1 kan tsarabobi iri iri domin bai wa iyayensa da iyayen matarsa da wasu danginsa abin kyauta."

A lokacin da Sinawa suke murnar wannan sabuwar shekara, su fi mai da hankali kan yadda za su yi ban kwana da tsohuwar shekara lokacin da suke murnar sabuwar shekara. Sabo da haka, ba ma kawai suna sayen kayayyakin masarufi ba, har ma suna sayen sabbin huluna da tufafi da sabbin na'urori masu aiki da lantarki a gida domin neman fatan alheri a sabuwar shekara. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China