in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kara sani kan dabbar Panda a birnin Chengdu
2010-02-10 13:56:13 cri
Masu karatu, barka da war haka! Tasallah ce ke yi muku marhabin cikin shirinmu na yawon shakatawa a nan kasar Sin. A ko wace ranar Talata mu kan zazzagaya kasar Sin tare.

Kasar Sin ce take da dabbar Panda a duk duniya baki daya. A kasar Sin, irin wannan dabba na matsayin dukiyar kasa. Yawan dabbobin Panda da suke rayuwa a dajin da ke lardin Sichuan a kudu maso yammacin kasar Sin ya wuce kashi 3 cikin kashi 4 bisa jimillarsu a duk fadin kasar. Lardin Sichuan na daya daga cikin wuraren da dabbobin Panda suke son zama. Ta haka, lardin Sichuan ya kafa sansanonin kiyaye dabbar da dama, inda ake kara yawan dabbar ta hanyar renonsu. Yau bari mu shiga sansanin nazari da renon dabbar Panda na birnin Chengdu, da zummar kara sani kan zaman rayuwar irin wannan kyakkyawar dabba.

Akwai dan yanayin sanyi a birnin Chengdu a lokacin hunturu, amma sanyi bai cika hana zuwan maziyarta masu yawa ga sansanin nazari da renon dabbar Panda a wannan birni ba. Da sassafe, mutane su kan yi jerin gwano mai tsawon mita 10 ko fiye a kofar sansanin. Wasu dalibai suna hira cikin zumudi yayin da suke cikin jerin gwanon. Inda suke cewa,"An ce, dabbar Panda ba ta fita, sai dai tana cikin farin ciki. Ina fatan yau za su yi farin ciki. Ta haka za mu iya ganin wasu."

"Ina matukar fatan ba za su yi barci ba a lokacin da muke kallonsu. Ina son in ga yadda suke cin abinci."

"E, haka ne. Ina fatan zan ga yadda suke wasa da kuma tsalle-tsalle."

"Ina matukar son taba su. Amma kada mu taba su."

Gorori masu kore mai haske sun rufe wannan sansani duka. A sakamakon kasancewa a kwarin manyan tsaunuka, sansanin nazari da renon dabbar Panda na Chengdu ya yi kama da babban wurin shan iska da aka gina a manyan tsaunuka. A bangarori daban daban a wannan wurin shan iska, akwai wurare da yawa da dabbar Panda ke rayuwa. Huang Jie, wadda ke yi wa maziyarta bayani a sansanin nazari da renon dabbar Panda na Chengdu ta yi karin bayani da cewa,"Idan mutane suna renon Panda a wani wuri maras fadi cikin dogon lokaci, halayyarsu za ta canja. Ta haka mu kan canza dakunansu a lokaci lokaci, za su iya nuna wa wuraren kwanansu sha'awa kullum. Haka kuma, mu kan samar musu wasu abubuwan wasa kamar lilo da kwallo da zummar kyautata zaman rayuwarsu, za su ji dadin zamansu."

Ko da yake ana sanyi, amma Panda suna wasa a waje. Wasu na mamaki da cewa, ko Panda ba su jin sanyi? Game da wannan, Huang Jie ta yi bayani da cewa,"Panda na son lokacin sanyi. Panda kan rayu a gandun daji na gora a manyan tsaunuka masu tsayin 1500 zuwa 3400, inda yanayin zafi ba ya wuce digiri 20 a duk shekara. Panda na da gashi mai yawa da fata mai kauri, sai ka ce suna sanye da tufafin maganin sanyi. Haka kuma, gumin da suke yi ba ya wucewa ta gashinsu, shi ya sa ba su jin sanyi ko kadan. Ko a lokaci mafi sanyi, ba su yi barci ba, su kan fita waje domin samun abinci."

Duk wanda ya taba ganin Panda yana ganin cewa, dalilin da ya sa Panda ta yi kiba shi ne domin suna sha'awar cin abinci da yin barci. Maziyarta da yawa sun gano cewa, wadannan dabbobi masu kiba kan kwanta a kasa tare da sanya gorori da yawa a kansu, suna cin gororin a tsanake. Huang Jie ta yi mana bayani da cewa, a ko wace rana, Panda kan kashe awoyi 16 ko fiye wajen neman abinci ko kuma cin abinci. Sauran awoyi 8 kuma, su kan yi barci. Ina dalilin da ya sa Panda ta kan dauki dogon lokaci domin cin abinci? Gorori nawa ne ta kan ci a ko wace rana?

Ashe! Yau shekaru miliyan 8 da suka wuce, an samu Panda a matsayin dabbar da ke dogara da cin nama. Amma sannu a hankali, sun mayar da gororin da aka iya samunsu a wurare da yawa, kuma gororin suna girma cikin sauri a matsayin abincinsu. Duk da haka, cikin Panda ba ya iya sarrafa gorori yadda ya kamata, saboda a da Panda dabba ce mai cin nama. Ta haka tilas ne su kan yi ta cin gorori domin samun isassun abubuwa masu gina jiki, tare kuma da rage motsinsu domin kiyaye karfinsu. Huang Jie ta ce,"A ko wace rana, Panda kan ci gororin da yawansu ya kai kilogram 20 zuwa 30. Ko da yake su kan ci gorori masu yawa haka, amma su kan jefar da yawancin gororin da suka ci da misali kilogram 10 ko fiye kai tsaye kamar kashi, dan haka tilas ne su kan yi ta ci domin samun isassun abubuwa masu gina jiki, tare da rage motsinsu. Gorori ba su kunshe da abubuwa masu gina jiki da yawa, amma Panda kan yi kiba kamar haka, wannan shi ne hanyar zaman rayuwarsu. Haka kuma, wannan shi ne daya daga cikin dalilan da suka sa suke kasancewa a duniya har zuwa yanzu."

Renon Panda shi ne wani muhimmin aiki a sansanin nazari da renon Panda na Chengdu. A sakamakon bukatun musamman, ba a bude kofar dakunan renon kananan Panda ga maziyarta. Maziyarta suna samun damar kallon kananan Panda ta tagar dakuna ne kawai. Huang Jie ta ce, a watanni da dama da suka wuce, karin mutane kan taru a gaban tagogin dakunan renon kananan Panda. Lalle yanzu ana renon Panda 2 jarirai da aka haife su a watan Satumba na bara. In an kwatanta su da Panda baligai, kananan Panda sun fi kyan gani da kuma sha'awar motsi. Wadannan Panda 2 jarirai suna ta rarrafawa a kan wani gado. Mai kiwonsu kuma yana tsayawa a dab da su, ya kan taba su kullum. Huang Jie tana mai cewar, Panda jarirai ba su iya yin kashi da kansu yadda ya kamata ba, ta haka masu kiwonsu na bukatar rika taba cikinsu da zummar taimaka musu sarrafa abinci. Huang ta ce,"Kullum Panda jarirai ba su kasancewa cikin koshin lafiya. Ta haka mai kiwonsu kan taba cikinsu domin taimaka musu yin kashi. Panda jarirai ba su iya yin kashi da kansu ba, Idan Panda mahaifiya suna renon 'ya'yansu da kansu, su kan taba cikin 'ya'yansu da harshe. Amma a yayin da mu mutane ne muke kiwonsu, mu kan taimaka musu da hannu."

Madam Zhang Man ta je Chengdu ziyara ne daga lardin Hubei. Ta taba kallon Panda baligai da yawa a gidajen dabbobi a birane da dama, amma a karo na farko ne ta ga irin wadannan kananan Panda. Sansanin ya samar wa Panda kyawawan sharuddan zaman rayuwa, ta haka ga alama Panda sun fi sha'awar motsi. Madam Zhang ta ce,"A da mu kan ga Panda a gidan dabbobi. Amma ga alama ba su sha'awar motsi kamar yadda wadanda muka gani a wannan sansani suke. Yau mun ga Panda jarirai da aka haife su ba da dadewa ba da kuma kananan Panda da kuma Panda baligai. Wannan sansani yana kiyaye Panda ta hanyar da ta dace har ma daga kananan fannoni. Haka kuma, Panda na da kyan gani matuka. Lalle gani ya kori ji!"

Jordan Mariuma da ya fito daga kasar Amurka ya kan yi yawo a wannan babban wurin shan iska na renon Panda a duk safe. Kallon Panda fiye da 20 ya faranta ransa kwarai da gaske. Sun ishe shi ainun. Jordan ya ce,"Panda na da kyan gani sosai. Ina farin ciki da ganin ana kula da su yadda ya kamata a nan kasar Sin. Yau a karo na farko ne na ga Panda da idona. Na ga Panda fiye da 20. Dukkansu na da matukar kyan gani. Ba zan iya dauke ido a kansu ba."

To, masu karatu, laifin dadi karewa. Ziyararmu a sansanin nazari da renon Panda da ke birnin Chengdu a yau ke nan. Tasallah da na shirya muku wannan shiri, nake cewa, ku huta lafiya, sai mako na gaba war haka, daga nan sashen Hausa na CRI.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China