in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jin dadin fahimtar kyan siffar kankara da dusar kankara a Harbin a lokacin hunturu
2010-02-10 11:33:38 cri
Masu karatu, barka da war haka! Tasallah ce ke yi muku "Sannu!" cikin shirinmu na yawon shakatawa a nan kasar Sin. Yau za mu je wani birnin da ya shahara ne saboda fasahar sassaka kankara da dusar kankara. Shi ne birnin Harbin, babban birnin lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin, wanda kullum cike yake da abubuwa masu ban sha'awa. A halin yanzu, lokacin hunturu ya yi. Wadanda ke zaune a Harbin suna fama da sanyi mafi tsanani. A wasu lokuta, zafin yanayi kan kai digiri 20 zuwa 30 ko fiye a kasa da sifiri. Amma a sa'i daya kuma, ana fi jin dadi a sakamakon bude shagalin kankara da dusar kankara da ake saba shiryawa a ko wace shekara.

Tun daga watan Janairu na ko wace shekara, masu yawon bude ido da suka fito daga sassa daban daban na duniya sun soma kai wa birnin Harbin ziyara domin kara fahimtar tsananin sanyi da fasahar sassaka kankara da dusar kankara mai ban sha'awa. Har ma wasu da suka fito daga kudancin kasar Sin sun fahimci abubuwan da ba su taba sani ba. Lv Hao da ya fito daga birnin Guangzhou da ke kudancin kasar Sin, wannan shi ne karo na farko da ya kai ziyara a birnin Harbin, inda ya ce,"Harbin birni ne na kankara. Ban taba jin tsananin sanyi kamar digiri 30 ko fiye a kasa da sifiri ba. Ina kasancewa kamar yadda nake kasancewa cikin wata almara."

An fara yin shagalin kallon fitilun da aka kera da kankara tun daga shekarun 1960 a wani wurin shan iska mai suna Zhaolin a birnin Harbin. Masu fasahar sassakar kankara sun yi amfani da kankarar da suka samu daga kogin Songhuajiang kai tsaye da kuma fitilu domin samar da fasahar fitilun kankara da suka sha bamban da saura. Masu fasahar da kuma wadanda suka yi fice a sana'o'in hannu sun sanya kankara ta zama abubuwa masu kyan gani da wannan baiwa tasu. Haka kuma, wuraren shan iska cike suke da fitilun kankara masu ban mamaki da kuma kankarar da ke kyalkyali.

A bana, birnin Harbin ya hada kai da shahararren kamfanin Disney na kasar Amurka domin samar da wurin nishadi da aka gina da kankara da dusar kankara, kuma yana nuna halin musamman na Disney. Yang Jie, shugabar hukumar harkokin yawon shakatawa ta birnin Harbin ta yi mana karin bayani da cewa,"A bana, wurin nishadi na Zhaolin ya mayar da labarun Disney a matsayin babban taken shagalinsa. Ya kafa wata duniya ta hanyar yin amfani da kankara da dusar kankara bisa halin musamman na Disney, wadda fadinta ya kai murabba'in mita dubu 80, kuma an yi amfani da kankara mai yawan cubic mita dubu 20 da dusar kankara mai yawan cubic mita dubu 10 gaba daya. Ban da wannan kuma, an samar da karin harkokin nishadi ta hanyar yin amfani da kankara da dusar kankara."

Wurin shan iska mai suna babbar duniya mai kankara da dusar kankara da aka gina kan kogin Songhuajiang, wurin nishadi ne mafi girma a duk duniya, wanda aka mayar da kankara da dusar kankara a matsayin babban takensa. A cikin wannan wurin shan iska mai fadin murabba'in mita dubu 500, akwai abubuwan fasaha fiye da dubu 2 da aka kera da dusar kankara da kankara. A duk lokacin da dare ya yi duhu, wadannan abubuwan fasaha na da kyan gani matuka a sakamakon haske da inuwa. Sun samu babban yabo daga wajen matafiya na gida da wajen kasar Sin.

Kevin, wani dan kasar Birtaniya ya dade ya san wannan babbar duniya mai kankara da dusar kankara. A wannan karo, duk iyalinsa mutum 6 sun je Harbin ziyara. Kevin ya gaya mana cewa,"Ina jin mamaki sosai. Na dade ina Alla-Alla wajen kallon wadannan abubuwa. Sun shaku cikin zuciyata."

Jean, matar Kevin ta ce,"Wannan na da matukar kyan gani! Ban iya ganewa yadda suka samar da wadannan abubuwa ba."

A ko wace shekara, a yayin shagalin kankara da dusar kankara da a kan yi a birnin Harbin, a kan shirya gasar sassakar kankara da dusar kankara, inda matafiya kan more da kallon abubuwan sassakar kankara da dusar kankara na matakin duniya.

Li Xingsuo, wani mai fasahar sassakar kankara ne da ya fito daga lardin Yunnan na kasar Sin. Wannan shi ne karo na 2 da ya shiga taron baje-koli na dusar kankara. Ya gaya mana ra'ayinsa kan fasahar sassakar dusar kankara. Yana mai cewa,"Fasahar sassakar dusar kankara ta iya nuna ainihin kyan siffar muhallin halittu. Abubuwan sassakar dusar kankara na da tsabta kuma fari fata matuka. Ana sanyi sosai a wurin, in matafiya sun je can, su kan ji kamar yadda suke cikin duniyar kankara suna jin dadin kallon kankara da dusar kankara a arewacin kasarmu da kuma kyawawan abubuwan sassakar dusar kankara."

Baya ga kallon abubuwan sassakar kankara da dusar kankara, matafiya suna iya morewa ido da wasan ninkaya a lokacin hunturu a Harbin, da zummar fahimtar jaruntaka da rashin jin tsaron shan wahala da wadanda suke zaune a arewacin kasar Sin suke nunawa. Yang Jie ta yi karin bayani da cewa,"A kogin Songhuajiang mai sanyi matuka, a ko wace rana, masu sha'awar wasan ninkaya a lokacin hunturu kan tsunduma cikin ruwan kogin mai matukar sanyi. Hakan ya ba mutane mamaki sosai. A ko wace rana da safe, a kan yi wasan ninkaya da tsunduma cikin ruwan sanyi daga wani dandamali da yin wasan dambe cikin ruwa mai tsananin sanyi a wurare 3 na wannan kogi. Matafiya suna iya kallonsu."

In an kwatanta su da wadanda suke zaune a wasu wuraren kasar Sin, matasan da ke zaune a birnin Harbin sun fi son yin aure a duniyar kankara da dusar kankara mai tsabta da fari fat matuka. A yayin shagalin kankara da dusar kankara da aka yi a wannan shekara, maza da mata 56 sun shirya bikin aure tare. Liang Yan, wata amarya daga cikinsu ta bayyana cewa, burinta shi ne yin bikin aure tare da sanya tufafin aure mai fari fat a cikin duniya mai fari fat. Tana son shirya wani bikin aure mai tsarki. Inda ta ce,"Zan haddace wannan kyakkyawan bikin aure da aka yi a yayin shagalin. Mun zabi wannan wuri ne domin yana da fari fat da tsabta kwarai da gaske. Yana da kyau ainun. Ina zumudi, har ma ban ji sanyi ba."

Baya ga kankara da dusar kankara, akwai gine-gine masu dogon tarihi da aka gina bisa salon gine-gine na kasashen yammacin duniya a birnin Harbin, yayin da aka iya ganin coci-coci na addinan Eastern Orthodox da Catholicism da kuma Kirista a ko ina a wannan birni. Wadannan gine-gine masu sigar musamman sun kayatar da birnin Harbin sosai. Ana mayar da wannan birni kamar "karamin birnin Paris a gabashin duniya" da "birnin Moscow da ke gabashin duniya". Masu karatu, in kun kai ziyara a birnin Harbin, baya ga jin dadin fahimtar kyan siffar kankara da dusar kankara, halin musamman da wannan birni ke da shi kan iya faranta rayukanku ta wata hanya ta daban.

To, maddala, masu karatu, lokaci ya kure, bari mu sa aya ga ziyararmu a yau. Tasallah ce da ta gabatar muku da wannan shiri, nake cewa, ku huta lafiya, sai mako mai zuwa war haka daga nan sashen Hausa na CRI.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China