in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana maraba da masanan kasashen waje domin aiki a nan kasar
2010-02-10 09:09:10 cri

Firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya bayyana a ran 9 ga wata a nan birnin Beijing cewa, yana maraba da masanan kasashen waje da su zo kasar Sin domin aiki da shiga aikin raya kasar Sin iri ta zamani.

Bisa labarin da gidan talibijin na kasar Sin ya bayar, an ce, a wannan rana, Wen Jiabao ya gana da masana da kwararrun kasashen waje da suke aiki a Sin da kuma iyalansu, inda Wen Jiabao ya ce, bude kofa ga kasashen waje muhimmiyar manufa ce ta kasar Sin, kana Sin tana nacewa ga jawo jarin kasashen waje da kuma masanansu. Ya kara da cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan manufar raya kasa ta hanyar shigar da masana da kwararru domin samun bunkasuwa mai dorewa, kuma tana nacewa ga neman bunkasuwar tattalin arziki ta hanyar yin amfani da kimiyya da fasaha, shi ya sa, dole ne a horar da masanan kasar Sin a yayin da ake shigar da masanan kasashen waje musamman ma mutanen da suka nuna kwarewa sosai a wasu fannoni.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
11:00 - 14:00 UTC Shirin Rana
Shiri na Yau Shiri na Jiya
15:00 - 18:00 UTC Shirin Yamma
Shiri na Yau Shiri na Jiya
16:30 - 17:30 UTC Shirin Maraice
Shiri na Yau Shiri na Jiya
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China