in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwa kan harkokin cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ya dace da samun babbar moriyar jama'ar Sin da Afrika
2010-02-09 20:09:35 cri
A ranar 9 ga wata, yayin da sakatare janar na cibiyar kula da harkokin mu'amala kan harkokin tattalin arziki na kasa da kasa a kasar Sin Wei Jianguo ke zantawa da wakilinmu, ya bayyana cewa, hadin gwiwa kan harkokin cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ya dace da samun babbar moriyar jama'ar Sin da Afrika, kuma ya dace da samun bunkasuwar kasashensu.

Wei Jianguo ya ce, bayan da aka yi taron koli kan sha'anin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, matsakaicin yawan cinikin bangarorin biyu tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ya kan karu da sama da kashi 40 cikin 100 a ko wace shekara. Mr. Wei ya yi nuni da cewa, yanzu, ana samun bunkasuwar cinikin bangarorin biyu cikin daidaito, kuma kayayyakin da Sin ta kan shigar da su daga kasashen Afrika sun dace da samun bunkasuwar kasar Sin, kana kasar Sin ita ma ta kan fitar da kyawawan kayayyaki masu araha da ke samun karbuwa ga jama'ar Afrika zuwa kasashen Afrika, an ce, hadin gwiwa kan harkokin cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika zai kawo sakamako na hadin gwiwa da samun moriyar juna. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
11:00 - 14:00 UTC Shirin Rana
Shiri na Yau Shiri na Jiya
15:00 - 18:00 UTC Shirin Yamma
Shiri na Yau Shiri na Jiya
16:30 - 17:30 UTC Shirin Maraice
Shiri na Yau Shiri na Jiya
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China