in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta fara tace sinadarin Urainium mai ingancin 20% a Natanz
2010-02-09 19:09:14 cri

A ran 9 ga wata, shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta Iran Ali Akbar Salehi ya shelanta cewa, a wannan rana Iran ta riga ta fara tace sinadarin Urainium mai ingancin kashi 20 cikin kashi dari a Natanz.

Malam Salehi ya bayyana cewa, Iran ta kara samun wani layin samarwa a Natanz, tare da kafa wata sabuwar na'urar tace sinadarin Urainium a can. Yanzu an riga an saka sinadarin Urainium mai ingancin kashi 3.5 cikin kashi dari a ciki, a kokarin samun sinadarin Urainium mai ingancin kashi 20 cikin kashi dari.

Malam Salehi ya furta cewa, kafin wannan, layin samarwar yana wurin. A kwanan baya, an kara ingancinsa. Game da ingantawar ta karshe kuma, za a yi shawarwari da hukumar IAEA.

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Iran Ramin Mehmanparast ya bayyana a wannan rana cewa, tace sinadarin Urainium mai ingancin kashi 20 cikin kashi 100 da Iran take yi bai saba wa makasudin yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana ba, kuma bai nuna cewa za a rasa damar yin shawarwari kan makamashin nukuliya a nan gaba ba.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
11:00 - 14:00 UTC Shirin Rana
Shiri na Yau Shiri na Jiya
15:00 - 18:00 UTC Shirin Yamma
Shiri na Yau Shiri na Jiya
16:30 - 17:30 UTC Shirin Maraice
Shiri na Yau Shiri na Jiya
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China