in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tabkin Qinghaihu, wuri ne da ake renon halittu
2010-02-09 16:38:34 cri

Masu karatu, barka da war haka! Tasallah ce ke yi muku "Sannu!" cikin shirinmu na yawon shakatawa a nan kasar Sin daga nan sashen Hausa na CRI. A bayyane take cewa, mu 'yan Adam da sauran halittu muna zaune tare a duniyarmu. Yau za mu je wani wurin da ake renon halittu mabambanta a nan kasar Sin.

Tabkin Qinghaihu na kasancewa tamkar wani lu'ulu'un da aka saka a tudun Qingzang. Ya zama na farko a tsakanin tabkuna guda 10 mafi kyan gani da mujallar yanayin kasa ta kasar Sin ta zaba. Shi ne kuma tabki mafi girma a nan kasar Sin. A yankin tabkin maras iyaka, ruwansa ya yi kama da ya hade da sararin sama tare, ana kuma iya ganin inuwar manyan tsaunukan dusar kankara a yankin tabkin. A cikin ruwan tabkin, kifaye da yawa suna rayuwa. A saman tabkin, dimbin tsuntsaye kan yi shawagi. A kewayen tabkin Qinghaihu kuma, akwai filin ciyayi mai launin kore, inda kuma ake samun rawayan furanni da kuma fararen tumaki masu yawa. Mazauna wurin 'yan kabilar Tibet da ta Mongolia su kuma mayar da tabkin Qinghaihu a matsayin tabki mai tsarki a zukatansu. A ko wace shekara, su kan shirya bikin nuna masa girmamawa da zummar samun alheri daga wajensa.

A ko wane watan Afrilu, a yayin da kankarar da ke cikin tabkin Qinghaihu ya narke, kuma ciyayi sun tsiro, bishiyoyi sun soma yin ganyaye a gabar tabkin, duban tsuntsaye masu yin hijira sun isa tabkin daga kudancin kasar Sin mai nisa, sun kafa shekunansu a tsibirin tsuntsaye da ke gabar arewa maso yammacin tabkin Qinghaihu, inda su kan saka kwai, su fara reno 'ya'yansu. A lokacin kaka, bayan da wadannan tsuntsayen masu yin hijira suka koma kudancin kasar Sin ba da dadewa ba, dimbin tsuntsayen ruwa masu siffar balbela wato Swan a Turance sun je tabkin Qinghaihu domin yin rayuwa a lokacin hunturu. A ganin Tan Li, wata jami'ar kula da harkokin yawon shakatawa ta gundumar Gangca ta lardin Qinghai, yanzu tabkin Qinghaihu ya kasance tabkin Swan zalla. Inda ta ce,"Galibi dai a farkon ko wane watan Oktoba, tsuntsayen Swan kan je tabkin Qinghaihu daya bayan daya. A shekarar 2005, akwai tsuntsayen Swan ba su wuce misalin 1500 kawai ba a tabkin Qinghaihu da kuma wuraren da ke dab da shi. Amma yanzu muna da su fiye da dubu 2. Muna iya ganin bakaken tsuntsayen Swan da wasu tsuntsayen da ba a iya ganinsu kullum a wasu wurare na daban."

A shekarun baya, an fadada wurare masu danshi a kewayen tabkin Qinghaihu, haka kuma, yawan idanun ruwa na ta karuwa, ta haka an samu karin dabbobi da tsirran da ke rayuwa cikin ruwa, ta yadda tsuntsayen Swan sue samun isasshen abinci da ruwa da kuma wuraren kwana. A ko wane lokacin hunturu, ana iya ganin tsuntsayen Swan suna tafiya da yin wasa a tabkin Qinghaihu. Kukansu ba ya iya karewa. A sararin sama da kuma tabkin da dukkaninsu suke da launin shudi, kyawawan tsuntsayen Swan biyu biyu su kan yi shawagi tare. Madam Tan ta kara da cewa,"A da, tsuntsayen Swan kan je tabkin Qinghaihu a watan Nuwamba, amma yanzu su kan je tabkin a watan Oktoba. Su kan je can da wuri-wuri har kwanaki 20 ko fiye. Dalilin da ya sa haka shi ne mun fi dora muhimmanci kan kare muhallin halittu a nan."

Kyawawan tsuntsayen Swan sun sanya tabkin Qinghaihu ya kasance tamkar a cikin tatsuniya. Haka zalika akwai wasu irin bareyi na musamman da ake iya samunsu a tabkin Qinghaihu kawai, wato Przewalski's gazelle a Turance, wadanda su kan yi gudu a filayen ciyayin da ke bakin tabkin sun samar wa wannan tabki karin suna.

Bareyi irin na Przewalski 'yan kanana ne, suna da sauri cikin harkokinsu, kuma suna da kyan gani sosai, musamman ma farin zanen da ya yi kama da zuciya da ke jelarsu ya fi jawo hankali sosai a lokacin da suke gudu a kan koren ciyayi. A zamanin da irin wannan kyakkyawar dabba ta taba rayuwa a jihar Mongolia ta Gida da jihohin Ningxia da Xinjiang da kuma lardin Qinghai da sauran wurare a kasar Sin. Amma a sakamakon kisan kiyashi na rashin tausayi da kuma mamaye wuraren kwanansu da mutane suka yi ta yi a cikin dogon lokaci, a tsakiyar shekarun 1980, babu wata barewa irin ta Przewalski da ke rayuwa a Mongolia ta Gida da Gansu da kuma Xinjiang. Yanzu akwai wasu da ba su wuce dari 6 kawai ba da ke rayuwa a wuraren da ke kewayen tabkin Qinghaihu.

A shiyyar kiyaye bareyi irin na Przewalski da aka gina a dab da tabkin Qinghaihu, a kan ga wasu bareyi irin na Przewalski da suke kasancewa cikin shiri, kuma suna da sauri cikin harkokinsu suna gudu da sauri. Ma Yuhai, wanda ke zaune a wurin, ya kan dauke hotuna tare kuma da darajanta irin wannan kyakkyawar dabba tamkar aljanun da ke rayuwa a tabkin Qinghaihu. Yana mai cewa,"Ga su wasu 60 ko fiye suna can misalin mita dari 3 ko fiye daga wajenmu. Wannan ya zama ruwan dare. Yanzu ana kiyaye muhallin wuraren da ke kewayen tabkin ta hanyar da ta dace. Bareyi irin na Przewalski sun fi samun zaman rayuwa na kwanciyar hankali. A shiyyarmu da muke kare su, a wasu lokuta, mu kan ga wasu fiye da dari 2. Yanzu akwai bareyi irin na Przewalski fiye da dari 6 a kewayen tabkin Qinghaihu."

Yanzu yawan tsuntsayen Swan na ta karuwa, haka ma, yawan bareyi irin na Przewalski su ma suna karuwa sannu a hankai ba tare da tangarda ba. Dalilin da ya sa haka kai tsaye shi ne kyautatuwar muhalli a tabkin Qinghaihu da kuma wuraren da ke kewayensa.

A shekarun baya da suka wuce, hukumar lardin Qinghai ta kiyaye da kuma kula da harkokin shiyyar yawon shakatawa ta tabkin Qinghaihu ta hanyar bai daya. Ta kuma zuba kudin Sin yuan miliyan 158 kan kare muhalli da kuma kula da harkokin tabkin Qinghaihu. Ren Jie, wani jami'in kula da harkokin kiyaye muhalli na lardin Qinghai ya gaya mana cewa,"Za mu fito da tsare-tsaren da abin ya shafa. Za mu hada wasu ayyukan da mabambantan hukumominmu suke gudanarwa tare. Muna nuna hazaka matuka. Mun yi imani da cewa, za mu iya ciyar da aikin kare muhallin tabkin Qinghaihu gaba."

A sakamakon kyautatuwar muhalli, kyakkyawan tabkin Qinghaihu kan ba mutane mamaki. Tun bayan lokacin zafi a bara, an ga tururi sau 3 a sararin tabkin Qinghaihu, wanda ba safai a kan gani ba. Chen Dehui, wani jami'in kula da harkokin shiyyar yawon shakatawa ta tabkin Qinghaihu ya bayyana mana ra'ayinsa game da wannan, inda ya ce,"Akwai wasu sharuddan muhalli na bullowar tururi. Musamman ma ana rana, ana ruwan sama amma a mabambantan lokuta. A bara, an fi samun ruwan sama da yawa a tabkin Qinghaihu bisa shekaru 2 da suka wuce. Ruwa mai tarin yawa ya taimaka wajen bullowar tururi. Dadin dadawa kuma, an yi ta kokarin fadada tabkin Qinghaihu, kuma an maido da fadin wurare masu danshi. Galibi dai, muhallin tabkin Qinghaihu ya samu kyautatuwa sosai."

A sakamakon kulawar da mutane suke nunawa a tsanake, kyakkyawan tabkin Qinghaihu mai ban mamaki ya ci gaba da nuna kyan surarsa. Yanzu tabkin Qinghaihu na da fuskar ruwa mai fadi. A sama da shi, dimbin tsuntsaye suna shawagi. A kewayensa kuma, tsuntsayen Swan na rayuwa cikin kwanciyar hankali. Bareyi irin na Przewalski na gudu cikin farin ciki. Kyakkyawan ruwan tabkin da sararin sama mai shudi kuma mai haske da farin gajimare da manyan tsaunuka da filayen ciyayi masu launin kore da ke kewayen tabkin dukkansu sun nuna wa mutane budaddiyar zuciyar da tabkin Qinghaihu ke da shi da kuma kyan surarsa, sun kuma nuna mana cewa, tabkin Qinghaihu zai kara samun kyan gani a nan gaba.

To, masu karatu, shirinmu na yau ke nan. Tasallah da na shirya muku wannan shiri, nake cewa, ku huta lafiya, sai mako na gaba war haka, daga nan sashen Hausa na CRI.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China