in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwakwa, alamar lardin Hainan
2010-02-09 14:48:11 cri
Masu karatu, barka da war haka! Tasallah ce ke yi muku marhabin a cikin shirinmu na yawon shakatawa a nan kasar Sin. Yaya yanayin Nijeriya da kuke ciki a halin yanzu? Yanzu haka dai, ana sanyi sosai a nan Beijing, hedkwatar kasar Sin. Kuma an riga ga saukar kankara mai laushi sau da dama a nan. Watakila mutanen kasashen Afirka da suke zaune a nan Beijing da ma arewacin kasar Sin baki daya wadanda suka zo ba da dadewa ba ba su saba da irin wannan sanyi ba, amma an riga an sani cewa, kasar Sin wata babbar kasa ce. Ko da yake ana tsananin sanyi a arewacinta, amma a kudancin kasar, sanyi ya dan lafa. Yau bari mu dan dumama jikinmu a kuryar kudu ta kasar Sin, wato lardin Hainan.

Tsibirin Hainandao tsibiri ne da ke kuryar kudu a nan kasar Sin. A kan kira shi tsibirin Yedao, ko kuma tsibirin kwakwa ta bakin Hausawa, saboda yana da yalwar bishiyoyin kwakwa. Birnin Haikou, babban birni ne a lardin Hainan birni na kwakwa a ganin mutane. Kwakwa halitta ce mafi nuna halin musamman na lardin Hainan, ta riga ta kasance alamar wannan lardi. In ka zo tsibirin Hainandao ziyara, to, tabbas ne za ka dandana kwakwa da bakinka domin jin dadin shan ruwan kwakwa da tuwon cikinta masu zaki da kamshi.

Da zarar ka sa kafarka a tsibirin Hainandao, bishiyoyin da za ka daga kai ka gani bishiyoyi ne na kwakwa kawai. Bishiyar kwakwa na da mikakken jiki da manyan ganyaye. Ko wace bishiyar tana kama da wata babbar budaddiyar laima. A duk shekara, bishiyoyin kwakwa suna yin 'ya'ya. A wasu lokuta, a kan wata bishiyar, ana iya ganin furannin kwakwa da 'ya'yan kwakwa kanana da tsoffi.

Siffar kwakwa ta yi kama da ta kankana. Kwakwar da ba ta nuna ba tukuna na da koren bawo, amma da ta nuna launinta ya zama mai ruwan kasa ne mai duhu. Kwakwa na hade da abubuwa masu gina jiki da yawa. Chen Qing, shugaban wata cibiyar masu ilmin abubuwan da kan gina jiki ta Hainan ya gaya mana cewa,"Kwakwa wani nau'in 'ya'yan itatuwa ne da ake samu a wurare masu zafi kawai. Haka kuma, ta fi sauran 'ya'yan itatuwan da ake samu a wurare masu zafi kyau. Kwakwar da ta kara nuna ta fi kunsar sinadarin furotin da mai. Ba za iya kwatanta sauran 'ya'yan itatuwan da ake samu a wurare masu zafi da kwakwa ba saboda sinadarin gina jiki da take da shi ya fi yawa. Sa'an nan kuma, ruwan kwakwa da tuwon cikinta na iya taimakawa wajen gina jikin mutane matuka."

Sinawa kan ce, kwakwa dukiya ce gaba daya. Dalili mafi muhimmanci da ya sa hakan shi ne domin a cikin duk wata kwakwa ba komai, sai ruwanta kawai. Bayan da kwakwar ta nuna, cike take da ruwa mai tsabta da zaki. Irin wannan ruwa na iya saukaka zafi da kishirwar da mutane kan ji. Wannan karamar kwakwa ta hada da dimbin abubuwa masu gina jiki a tuwon cikinta da kuma ruwanta.

Cao Sha, ta kai ziyara a Hainan daga lardin Sichuan, tana matukar sha'awar cin tuwon cikin kwakwa. Ta gaya mana cewa,"Tuwon cikin kwakwa garas-garas yake da kuma kamshi da dandano. Bayan da ka tauna tuwon cikin kwakwar, ta kan yi saura a bakinka, amma bayan da ka hadiye ta, sai ka ce ka hadiye gyada."

A lokacin tsananin zafi, a karkashin dogayen bishiyoyin kwakwa dake bakin teku, kana iya more ido da kyan surar teku tare da more baki da ruwan kwakwa, kana iya kece raini sosai. Haka zalika, kwakwa kan iya taimakawa mutane sosai kamar yadda magani ya kan yi. Bisa likitancin gargajiya na kasar Sin, an ce, tuwon cikin kwakwa da ruwanta suna iya warka da ciwon mutane ta mabambantan hanyoyi. Mr. Chen Qing ya yi karin bayani da cewa,"Kwakwa ta hada abubuwa masu gina jiki masu tarin yawa. Bisa likitancin gargajiya na kasar Sin, tuwon cikin kwakwa mai zaki kan iya karfafa saifa da tumbi. Ruwan kwakwa mai zaki kuwa kan iya samar da karin miyau da fitsari."

An ce, yawan man da ke cikin tuwon kwakwa ya kai kashi 35 cikin dari. Bawonta na kunshe da sinadarin Hydrocyania Acid da na Fiber da na lignin da dai sauransu, ta haka a lokacin da kake tauna tuwon cikin kwakwa, kana iya ji kamar kana tauna irin abu kamar katako. Duk da haka, tuwon cikin kwakwa na ba da taimako wajen gina jiki da kyautata fuska da shawo kai da kuma yin rigakafin ciwon fata da kuma karfafa saifa da tumbi.

To, yaya ruwan kwakwa fa? Ya zuwa yanzu ruwan kwakwa abin sha ne mafi yawan sinadarin amino acid a duk duniya, wanda ba mutane suka samar da shi ba. Sakamakon nazari ta fuskar likitanci ya shaida mana cewa, ruwan kwakwa na iya yin rigakafin ciwon zuciya da amosanin gabbai da ciwon kansa. A maimakon zama mai kiba, shan ruwan kwakwa kullum na iya rage yawan mai da ke cikin jinin mutum da yin rigakafin matsalolin jini na jikin mutum, ta haka ana iya tattalin lafiyar zuciyar mutum.

Mr. Chen ya gaya mana cewa, ana iya dafa abinci masu dandano mabambanta da kwakwa. Inda ya ce,"Muna iya dafa mabambantan abinci da kwakwa. Kullum a kan dafa kwakwa tare da kaji."

Abincin da mazauna lardin Hainan su kan dafa da kwakwa da kaji abinci ne da ake iya dandanawa a Hainan kawai, suna iya gina jikin mutane kwarai da gaske. Wani nau'in miyar da ake dafa wada kwakwa da kaji na iya karfafa saifa da tumbi, musamman ma wadanda ba su son cin abinci, su kan ji gajiya, ko kuma su kasance sirara. Wadanda ba su kamu da wani ciwo ba kuma, in suna ci, za su iya kara samun kyan jiki da kuma kara son cin abinci.

Ko da yake kwakwa na da matukar kyau, amma wasu ba su dace da cinta da yawa ba. Chen Qing ya ba da shawarar cewa,"Wadanda su kan ji zafi sosai a cikinsu ba su dace da cin kwakwa da yawa ba. Haka kuma, idan ka dade ba ka yi barci cikin lokaci a dare ba, kana son cin soyayyen abinci, ka kan ji fushi, ka kuma ji kishirwa a baka, kada ka ci kwakwa da yawa."

A birnin Haikou, ana sayar da kwakwa a wasu kofofin shaguna, alal misali, ana iya sayen kwakwa daya da kudin Sin RMB ko Yuan 2 ko 3 kawai a shagunan sayar da jaridu da mujalloli a kusa da tasoshin bus. Mai shagon zai yanke saman kwakwa, ya tura wani tsinke na tsotso cikinta, inda za ka iya jin dadin zakin ruwan kwakwar, bayan da ka shanye ruwan kwakwar, mai shagon zai fasa kwakwar zuwa bangarori da dama, ya ba ka wani cokali, to, yanzu kana iya cin tuwon cikin kwakwar.

A lokacin da kake yawo a titi a birnin Haikou, bishiyoyin kwakwa dake gefunan titin su kan yi kama da budaddun laima da dama, wadanda suka rufe hasken rana. Tare da iska, ganyayen bishiyoyin kwakwa na karkadawa. In ka gaji, to, kana iya shiga wani shagon da ke gefen titi, ka sayi wata kwakwa, kana iya shan ruwan kwakwa domin kawar da kirshirwa tare da yin hutu kadan, haka kuma, ruwan kwakwar ka iya kyautata jikinka a sa'i daya.

To, masu karatu, ziyararmu a tsibirin Hainandao da ke kuryar kudu a kasar Sin ke nan. Da fatan kun fahimta, Tasallah nake shirya muku wannan shiri, tare da fatan ku huta lafiya, sai mako na gaba war haka daga nan sashen Hausa na CRI.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China