in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kyakkyawan garin Heshun a lardin Yunnan
2010-02-09 14:34:27 cri
Masu karatu, barka da war haka! Tasallah ce ke yi muku marhabin a cikin shirinmu na yawon shakatawa a nan kasar Sin. Kamar yadda mu kan saba yi a ko wace ranar Talata, yau za mu zagaya kasar Sin tare. A yankin bakin iyakar lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin da kasar Myanmar, akwai wani tsohon gari mai tsawon shekaru kimanin dari 6, sunansa shi ne Heshun. To, bari mu fara ziyararmu a wannan kyakkyawan gari!

Garin Heshun na kasancewa a gundumar Tengchong ta birnin Baoshan na lardin Yunnan. In ka bi hanya mai fadi kuma maras gangare daga cibiyar gundumar Tengchong zuwa kudu maso yamma, bayan ka ratsa gonakin da ake noman shimkafa mai launin kore da kuma rafukan da ke karkata, sai ka iya ganin gidaje layi-layi da mazauna wurin suka gina a gangarar dutse. Wannan shi ne garin Heshun.

Da zarar ka shiga garin Heshun, kana iya fahimtar halin musamman na gargajiya da kwanciyar hankali maras hayaniyar birane a garin. A wannan tsohon gari, tituna sun hada tsoffin gidaje masu farin bango da bakin rufi da gidajen girmamawa magabata da manyan kofofin nuna girmamawa masu kyan gani da hasumiyoyi masu kayatarwa tare. Sa'an nan kuma, akwai bishiyoyi masu launin kore da dama a garin Heshun, mazauna wurin kan zauna a kan kujerun duwatsu da ke gindin bishiyoyin, inda su kan yi hira ko kuma jin dadin hutawa. A wajen garin Heshun, a wasu lokuta, tsuntsayen Egret wato Bailu a bakin Sinawa kan yi tafiye-tafiye tare da ratsawa gonakin da ake noman shimkafa. A cikin 'yan tabkuna kuma, ana iya ganin kyawawan furannin Lotus da yawa. Tsoffi kan yi fatsa a cikin inuwar bishiyoyin Willow. Dukkan wadannan abubuwa kan faranta rayukan mutane sosai.

A garin Heshun, ana iya samun wani nau'in gini mai sigar musamman, wanda kuma ke iya dumama zukatan mutane sosai, wato hasumiyar Xiyiting, ko kuma hasumiyoyin wanke tufafi a bakin Hausawa. In an tabo magana kan wadannan hasumiyoyi, to, tilas ne a ambaci tarihin Heshun a matsayin garin Sinawa mazauna kasashen waje. Heshun da ke kasancewa a bakin iyakar kasar tana makwabtaka da kasar Myanmar. A zamanin da, maza kan yi ciniki a kudancin Asiya da kudu maso gabashin Asiya. Wadanda suka bar garinsu suna begen iyalansu matuka. Da fatan kare matan da suka wanke tufafi daga iska da ruwan sama, wasu sun ba da kyautar kudi, sun gina hasumiyoyin wanke tufafi masu siffofi daban daban a bakin kogi yau shekaru 100 ko fiye da suka wuce.

Dogon lokaci ya wuce. Ko da yake wadanda suka gina hasumiyoyin sun riga mu gidan gaskiya, amma har zuwa yanzu ana iya jin amon wanke tufafi a wadannan hasumiyoyi. Kamar yadda magabatansu suka taba kasancewa suna yi, mazauna wurin suna ci gaba da bin hanyar zaman rayuwa ta gargajiya a garin Heshun. Mata kan wanke tufafi tare a cikin hasumiyoyin. Zhao Xiuxing, wadda ke zaune a garin ta gaya mana cewa, ko da yake ta sayi injin wanke tufafi, amma tana son wanke tufafi a hasumiyoyin wanke tufafi. Inda ta ce,"A ko wace rana, na kan wanke tufafi a nan. Ko da yake na iya yin amfani da injin wanke tufafi a gida, amma injin yana jan wutar lantarki da kuma garin sabulun wanke tufafi da yawa. A hasumiyar wanke tufafi, baya ga wanke tufafi, na iya yin hira da abokaina."

Mazauna garin Heshun sun hada gudanar da aikin gona da harkokin ciniki da kuma koyon ilmi tare. Ba su daina neman ilmi daga zuriya zuwa zuriya ba. A wannan karamin gari, an gina dakin karatu na Heshun, wanda ya fi tsufa da girma a yankunan karkara a kasar Sin. Yanzu a cikin dukkan mazauna garin Heshun fiye da dubu 6, wasu fiye da dubu 3 suna da katunan karanta littafi na wannan laburare. Cun Maohong, shugaban laburaren ya yi mana karin bayani da cewa,"A cikin daruruwan shekaru da suka wuce, kakannin-kakanninmu sun gano cewa, ba za a iya ciyar da garinsu gaba da kuma wadatar da zuriyoyin baya ba, sai dai an ilmantar da mutane. Ta haka a shekarar 1928, an gina dakin karatu na Heshun, kuma a shekarar 1940, an kaddamar da makarantar midil ta Yiqun."

A cikin dakin karatu na garin Heshun, wani mazaunin garin mai suna Liu Fuqing yana karanta jaridu, ya gaya mana cewa, wannan dakin karatu, wuri ne da ya kan yi karatu. A ko wace rana, ya kan je wajen domin karanta jaridu da dudduba bayanai bayan aiki. Yana ganin cewa,

"Muna yayata raya zaman al'umma mai jituwa a halin yanzu, amma yau daruruwan shekaru da suka wuce, a yayin da aka kafa manyan kofofin nuna girmamawa a garinmu, an gabatar da irin wannan tunani. A garinmu na Heshun, muna sa muhimmanci kan ladabi. Mazauna wurin na da kyakkyawar halayya a sakamakon tasirin da laburaren Heshun ke yi musu. Suna da kirki sosai."

Ni'imtaccen muhalli da mutane masu kirki da kyakkyawan yanayi ta fuskar al'adu dukkansu sun jawo karin matafiya da su je garin Heshun ziyara. Mr. Zhang ya je Heshun daga lardin Sichuan ya bayyana cewa, ko da yake ba a bude kofar garin Heshun ga matafiya cikin dogon lokaci ba, amma an aza harsashi mai inganci ta fuskar al'adu a nan. Garin ya dace da matafiya sosai. Inda ya ce,"Babu kananan garuruwa da yawa da suka gina wani laburare mai yawan littattafai kusan dubu 80. An dade ana adana wadannan littattafai yadda ya kamata, hayakin yaki bai iya yi musu barna ba. Wannan ya nuna cewa, zuriyoyin al'ummar Sin na gadon al'adu yadda ya kamata. Sa'an nan kuma, a garin, akwai ni'imtattun wurare. Ana kuma iya ganin dutse mai aman wuta da magangarar ruwa da idon ruwa mai zafi a wannan karamin gari. Kada mu manta da mazauna gundumar Tengchong masu kirki."

Ya zuwa yanzu zuriyoyin mazauna garin Heshun suna zaune a gidajen da suka gina da tubali da katako. Raya tsohon garin ya haifar da wata matsala, wato shin karuwar yawan matafiya za ta kawo illa ga zaman rayuwar mazauna wurin? Yin Shaobo, wani jami'in kula da harkokin yawon shakatawa na wurin yana mai ra'ayin cewa,"Tun zamanin da, wadanda suke zaune a garin Heshun kan nuna budaddiyar zuciya, suna da wayin kai sosai. Wasu kan yi koyi da saura. Su kan yi koyi da al'adun kasashen waje. Idan masu yawon shakatawa sun zo garinmu ziyara, to, za su kawo mana al'adu na zamani da tunanin zamani, ta haka mazauna garinmu za su samu damar fahimta da kuma koyon al'adun zamani. Wannan abu mai kyau ne, haka kuma, wata kyakkyawar dama ce. Mazauna garinmu ba su ganin cewa, masu yawon shakatawa sun kawo illa ga zaman rayuwarsu."

Lalle wannan gaskiya ne! Al'adun garin Heshun na hade da abubuwa daban daban. Mabambantan al'adu suna kasancewa tare cikin jituwa a garin Heshun. Al'adun gargajiya mabambanta da ni'imtattun wuraren da suka sha bamban da saura sun sanya garin Heshun ya zama kyakkyawan wurin da ba za a iya kyale shi ba a kudu maso yammacin kasar Sin.

To, maddala, masu karatu, ziyararmu a karamin Heshun da ke kudu maso yammacin kasar Sin a yau ke nan. Tasallah da na shirya muku wannan shiri nake cewa, ku huta lafiya. Sai mako na gaba war haka daga nan sashen Hausa na CRI. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China