in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Macao tana yayata kanta ta hanyoyi daban daban a matsayin birnin yawon shakatawa
2010-02-09 14:29:18 cri
Masu karatu, barka da war haka! Tasallah ce ke yi muku "Sannu!" a cikin shirinmu na yawon shakatawa a nan kasar Sin. A ko wace ranar Talata, mu kan zagaya kasar Sin tare. A kwanan baya, yankin musamman na Macao na kasar Sin ya jawo hankali sosai a sakamakon cika shekaru 10 da aka maido da mulkin kan wannan yanki ga hannun gwamnatin kasar Sin. Saboda haka, yau za mu je wannan yanki tare domin kara saninsa.

An Dongliang, shugaban hukumar aikin yawon shakatawa ta yankin musamman na Macao ya sha bayyana a wurare da dama cewa, hukumarsa tana kokarin sa kaimi kan samun karin mabambantan matafiya da kuma samar da karin hanyoyin yawon shakatawa daban daban.

Kafin maido da Macao s hannun gwamnatin kasar Sin, galibin matafiyan da suke zuwa Macao ziyara, mutane ne da suka fito daga wani yankin musamman na daban na kasar Sin wato Hong Kong. A shekarar 1999, yawan mutanen da suka je Macao ziyara daga sassa daban daban na gida da wajen kasar Sin ya wuce mililyan 7 da dubu 440. Amma a watan Yuli na shekarar 2003, an saukaka wa wadanda suke zaune a babban yankin kasar Sin kai wa Hong Kong da Macao ziyara, ta haka a ko wace shekara yawan matafiyan da suke zuwa Macao ziyara daga babban yankin kasar Sin na ta karuwa. A shekarun baya, irin wannan adadi ya wuce rabin jimillar wadanda suka je Macao ziyara. A shekarar 2008, mutane kimanin miliyan 22.9 da suka fito daga sassa daban daban na gida da wajen kasar Sin sun je Macao ziyara, wadanda yawansu ya ninka sau 2 ko fiye bisa na kafin shekarar 1999. Yanzu ko da yake halin da ake ciki a fannin yawon shakatawa a duniya ba ya iya faranta rayukan mutane sosai, amma Macao na maido da yadda ta taba kasancewa a da. Mr. An Dongliang ya gaya mana cewa,"Ga alamar farfado da aikin yawon shakatawa na yankin musamman na Macao. Macao tana nan tana fita daga mawuyacin halin da rikicin kudi na duniya da kuma cutar murar A(H1N1) suka haifar. A watanni 3 da suka wuce, yawan matafiyan da suka zo Macao ziyara na ta karuwa sosai. Sa'an nan kuma, mun ga alamun farfado da tattalin arziki a sauran fannoni. Muna sa ran ganin za a ci gaba da farfado da aikin yawon shakatawa."

A shekarar 2002, hukumar yankin musamman na Macao ta fara mika wa hukumar tarbiya da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO rokon mayar da birni mai dogon tarihi na Macao a matsayin abun tarihi ta fuskar al'adu na kasa da kasa. A sakamakon kokari na tsawon shekaru 3, kwamitin kula da abubuwan tarihi na duniya a karo na 29 na hukumar UNESCO ya yi kudurin shigar da birni mai dogon tarihi da aka samu a Macao cikin "tarkadar sunayen abubuwan tarihi na kasa da kasa" a matsayin abun tarihi ta fuskar al'adu na duniya. Ta haka gine-gine masu dogon tarihi da aka samu a Macao, suka nuna halin musamman na al'adun kasar Sin da na yammacin duniya kuma sun zama abun tarihi na 31 a nan kasar Sin.

Birni mai dogon tarihi da aka samu a Macao birni ne mafi tsufa kuma mafi girma da haduwa a nan kasar Sin a halin yanzu, wadanda aka gina bisa salon gine-gine na kasar Sin da na yammacin duniya. A wannan birni mai dogon tarihi, tsohon bangare ya kasance cibiyarsa, kuma filaye masu makwabtaka da sshi da tituna sun hada sauran bangarori tare. A nan ana iya samun tsoffin gine-gine 20 ko fiye.

A shekarun baya, hukumar aikin yawon shakatawa ta yankin musamman na Macao da sana'o'in yawon shakatawa da na sufurin jirgin sama na wurin sun hada kai sun samar da hanyoyin yin yawon shakatawa domin kara fahimta kan abubuwan tarihi ta fuskar al'adu a Macao. an shimfida sabbin hanyoyin jirgin sama a Macao, ba tare da bata lokaci ba an yayata su ta fuskar aikin yawon shakatawa, an soma yi wa sauran sassan kasar Sin da kasashen ketare karin bayani kan Macao da ke da abubuwan tarihi ta fuskar al'adu masu nau'o'i daban daban.

A Macao, yau shekaru 400 ko fiye da suka wuce, an fara yin mu'amala ta fuskar al'adun kasar Sin da na yammacin duniya. A wurin, ana iya ganin tsoffin gidajen gargajiya da tsoffin gidajen ibada da aka gina yau shekaru dari 2 zuwa dari 3 da suka wuce, da gine-ginen da aka gina bisa salon gine-gine na kudancin Turai, da coci-cocin da aka gina bisa salon gine-gine na Baroque, da kuma gine-ginen zamani masu kyan gani. Dukkan wadannan gine-gine mabambanta sun shiga zukatan wadanda suke zaune ko kuma yin aiki ko yin bulaguro a Macao daga sauran wurare.

Mr. Liu ya yi shekaru 4 da wani abu yana aiki a Macao. Wannan wuri ya burge shi sosai. Liu ya ce,"Na yi shekaru 4 ko fiye ina aiki a Macao. A da, ban san Macao sosai ba, sai dai aikin yin caca da gidan ibada ma Magemiao. Amma bayan da na fara yin aiki a nan, na gano abubuwa da yawa da ban san su a da ba a wannan karamin birni mai halin musamman na al'adun kasar Sin da na yammacin duniya. Haka kuma, a kan shirya harkokin murnar bukukuwan gargajiya a Macao a ko wace shekara. Baya ga bikin Bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin da bikin Duanwu a ran 5 ga watan Mayu bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin da bikin Zhongqiu a ran 15 ga watan Agusta bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, mazauna Macao su ma su kan yi murnar Kirsimati da sauran bukukuwan kasashen yammacin duniya. Wadanda suke zaune a Macao kan ji dadi matuka. Haka zalika, abincin da ake samarwa a Macao ya sha bamban da saura. Baya ga wasu abinci mai dandano da Sinawa kan dafa, ana iya dandana wasu nau'o'in abinci mai dadi da aka dafa su ta hanyar da mutanen kasar Portugal suke bi. Saboda haka, wadanda suke zama a Macao da wadanda suka je Macao ziyara dukkansu na iya more bakinsu da abinci mai dandano."

A cikin shekaru 10 da suka wuce bayan da aka maido da Macao a hannun gwamnatin kasar Sin, hukumar Macao ta yi ta yin amfani da kuma kiyaye albarkatun yawon shakatawa da taka mallaka. A ko wace shekara ta kan shirya kasaitattun shagulgulan wasannin motsa jiki da na al'adu na duniya mabambanta da zummar yayata Macao da sanya Macao ta kara shahara da kuma jawo karin matafiya. Hukumar Macao ta kuma mayar da "Macao ta sha bamban da sauran wuraren duniya" a matsayin babban takenta. Ta hanyar "kara fahimta kan Macao", tana kokarin nuna halin musamman na Macao ta fuskar gargajiya da zamani.

To, yaya ra'ayoyin matafiya fa? Shin suna jin dadin yin ziyara a Macao? Ga wani matafiyin da yake ziyara a Macao daga lardin Shandong, yana mai cewa,"Macao na da kyau kwarai! Na yi kwanaki da dama ina ziyara a nan. Abinci da abun sha dukkansu na da matukar kyau. Ina jin dadin ziyara a nan. Haka kuma, mazauna Macao suna da kirki. Na ji an ce, za a shirya gasar tseren motoci ba da dadewa ba. An riga an shimfida hanyoyin tsere-tsere. In mun san wannan, za mu dakatar da ziyararmu. Ta haka za mu iya kallon gasar. Bayan da na koma gida, zan yi wa abokaina karin bayani kan Macao."

Ko wane watan Oktoba zuwa na Nuwamba, lokuta ne mafi dacewa ga matafiyan da su kan kai wa Macao ziyara. Wadanda su kan je Macao ziyara daga sassa daban daban na duniya kan iya more kallon wasannin wuta masu launuka daban daban da aka nuna da gasar tseren motoci mai ban sha'awa da fitattun 'yan wasa na kasa da kasa suka yi, tare kuma da more bakinsu da abinci mai dandano masu halin musamman na kasa da kasa.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China