in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tabkin Qinghaihu, tabki ne mafi kyan gani a kasar Sin
2010-02-09 14:08:57 cri
Masu karatu, barka da war haka! Tasallah ce ke yi muku marhabin a cikin shirinmu na yawon shakatawa a nan kasar Sin. A ko wace ranar Talata, mu kan zagaya kasar Sin tare. Yau za mu sa kafarmu a tudun Qingzang, wato wani yanki mai ban mamaki a nan kasar Sin, da zummar kara fahimta kan tabkin Qinghaihu, daya daga cikin tabkuna mafi kyan gani a kasar Sin.

Tabkin Qinghaihu na cikin kwarin Qinghaihu da ke arewa maso gabashin lardin Qinghai. Yana da nisan kilomita 151 a tsakaninsa da birnin Xining, babban birnin lardin Qinghai. Hanyar mota mai lamba G109 da kuma hanyar dogo ta Qingzang da sauran hanyoyi sun ratsa kwarin Qinghaihu, ta haka ana samun saukin zuwa wurin.

Tabkin Qinghaihu a bakin 'yan kabilar Tibet shi ne Mtsho-sngon, 'yan kabilar Mongolia kuma kan kira shi "Kokonor", ma'anar wadannan sunaye 2 a bakin 'yan kabilar Han ita ce teku mai launin shudi kamar yadda sararin sama ke kasancewa. Li Yucai, wani mai jagorantar maziyarta a wurin ya yi karin bayani da cewa, mazauna wurin ba su taba ganin teku ba, shi ya sa a ganinsu, tabkin Qinghaihu ya yi kama da teku, ta haka, su kan kira shi "Xihai", wato teku na yamma. Li ya ce,"An zabi Tabikin Qinghaihu a matsayin tabki mafi kyan gani a kasar Sin, kuma shi ne tabki mai ruwan gishiri mafi girma da aka samu a yankuna marasa mafitar teku a nan kasar Sin. Dalilin da ya sa haka shi ne babu mafita a wannan tabki, ruwan bai iya fita waje ba. Fadin tabkin ya kai murabba'in kilomita 4500 gaba daya, ya fi rabin fadin birnin Xining yawa. Tsayin da ke tsakanin fuskar tabkin da leburin teku ya kai mita 3196. Fadin tabkin ya kai kilomita 106 daga gabas zuwa yamma, fadinsa daga kudu zuwa arewa ya kai kilomita 63. A kewayen tabkin, akwai manyan tsaununka, wadanda tsawonsu ya kai kilomita 360. Ban da wannan kuma, matsakaicin zurfin ruwa ya kai mita 19, yayin da a wasu bangarori tabkin, zurfin ruwan ya kai mita 39."

A kewayen tabkin Qinghaihu, akwai filayen ciyayi masu fadi matuka. A dab da bakin tabkin, babu tudu babu gangare. Isasshen ruwa da yanayin rashin sanyi a wurin sun sanya wuraren da ke dab da bakin teku sun kasance dausayi mai kyau. In an tsaya a bakin tabkin Qinghaihu, sai a gano cewa, manyan tsaunuka masu launin kore suna kewayen tabkin, kamar yadda mahaifiya ta rungumi yaranta. Ana iya ganin hasken rana a fuskar ruwan tabkin mai launin shudi kuma mai tsabta. A filin ciyayi mai launin kore, tumaki masu launin fari suna kasancewa tamkar gajimare. A fuskar ruwan tabkin da ba a iya ganin iyakarsa ba, ana iya ganin manyan tsaunuka na kankara mai laushi. A cikin tabkin kuma, akwai kifaye da yawa. A sama da tabkin kuwa, tsuntsaye suna tafiya.

A gindin tabkin Qinghaihu, akwai tudu da gangare, haka kuma, halayen musamman na ruwan tabkin ya sha bamban, haka zalika, yanayi kan samu sauyawa a sakamakon mabambantan lokuta, ta haka ko a rana daya, launin ruwan tabkin Qinghaihu ya kan sha bamban, ba a iya kiyastawa ba. Wannan ya ba mutane mamaki matuka. Mr. Li Yucai ya ce,"Kullum ana iya ganin launuka guda 7 a tabkin Qinghaihu. Ta haka, mazauna wurin 'yan kabilar Tibet kan kira wannan tabki da sunan 'tabkin Qicaihu'. Kuma a zukatansu, wannan tabki na matsayin tabki mai tsarki. A ko wane watan Yuli, tabkin Qinghaihu ya fi kyan gani. A bakin tabkin, tsirran Rape sun fid da fure sosai. Sararin sama mai launin shudi da gajimare mai launin fari da kuma furannin Rape masu launin rawaya dukkansu na da kyan gani kwarai da gaske."

A lokacin hunturu fa, iska mai matukar sanyi ta buga da karfi, har ma manyan tsaunuka da kuma filin ciyayi sun zama na rawaya mai duhu. A wasu lokuta, bayan da aka yi kankara mai laushi, sun yi kama da sanya tufufi masu launin azurfa. A ko wane watan Nuwamba, tabkin Qinghaihu ya fara daskarewa. Fuskar tabkin mai launin shudi ta zama na launin azurfa gaba daya, ta yi kama da wani babban madubi. A karkashin hasken rana, wannan babban madubi ya kan yi walkiya a ko yaushe.

A duk lokacin zafi da na kaka, lokuta ne mafi dacewa wajen yin bulaguro a tabkin Qinghaihu. Mr. Wang Feng ya je tabkin Qinghaihu ziyara daga lardin Shaanxi. A cewarsa, zuwa tabkin Qinghaihu burinsa ne na dogon lokaci. Inda ya ce,"Na ji an ce, lardin Qinghai na da kyan gani sosai, inda akwai kyakkyawan tabkin Qinghaihu, da gidan ibada na Taersi. Na ji farin ciki sosai da zuwa nan. Cike nake da murna da ganin sararin sama mai launin shudi da tabkin mai launin shudi mai haske da kuma manyan tsaunuka masu launin kore. Abokan da ke zaune a lardin Qinghai dukkansu suna da kirki ainun. Sa'an nan kuma, muhalli a nan na da kyau kwarai da gaske. Mazauna wurin mutane ne masu son karbar baki da hannu bibbiyu. Ni'imtattun wurare da iska mai ni'ima na dacewa da yin bulaguro da kuma kwana."

A tabkin Qinghaihu akwai kananan tsibirai guda 5, wadanda suka yi kama da kananan kwale-kwale guda 5 a tabkin. Mabambantan siffofinsu sun fito da kyan ganinsu daban daban. A cikin wadannan kananan tsibirai 5, tsibirin tsuntsaye wato Niaodao ya dade yana shahara. Fadinsa ya kai murabba'in kilomita 0.5 kawai, amma a ko wane lokacin bazara da na zafi, tsuntsaye fiye da dubu 100 sun yada zango a kan wannan karamin tsibiri. Tafiye-tafiyen da dubu duban tsuntsaye su kan yi tare na da kyan gani sosai.

Tabkin Qinghaihu ba kawai wani wurin yawon shakatawa ne mai ban mamaki ba, har ma wani babban tabki ne da ke samar da albarkatu da yawa, kuma masu nazarin kimiyya daga sassa daban daban na duniya sun mai da hankali a kai. Gwamnatin kasar Sin ta taba yin cikakken bincike sau da dama a kan tabkin Qinghaihu, inda ta gano albarkatun ma'adinai masu tarin yawa a cikin wannan tabki. Ban da haka kuma, tabkin yana da yalwar kifayen Huangyu. Shi babban wurin renon kifaye ne mafi girma da ba mutane suka kafa ba a arewa maso yammacin kasar Sin.

A bakin tabkin Qinghaihu, 'yan kabilar Han da ta Tibet da ta Mongolia da ta sauran kananan kabilu suna zama tare cikin jituwa. Suna kiyaye da raya da kuma yin amfani da wannan babban tabki mai fadi, wanda yake kawo musu alheri kullum. Sa'an nan kuma, kyan surar tabkin Qinghaihu kan jawo hankalin dubu dubatan matafiya na gida da na kasashen waje. Ta haka hukumar yawon shakatawa ta lardin Qinghai ta kafa wurin shan iska a tabkin Qinghaihu da zummar bunkasa aikin yawon shakatawa a tudu, wanda ya fara samun karbuwa. A wurin shan iska da ke tabkin Qinghaihu, matafiya suna iya jin dadin kallon ni'imtattun wurare a dausayin da ke kan tudu, haka kuma, suna iya yin yawo a filayen ciyayi da kuma hawan tudun rairayi a kan dowaki da sa. Dadin dadawa kuma, suna iya kai ziyara a gidajen makiyaya domin kara sanin al'adun gargajiya na makiyaya 'yan kabilar Tibet da ta Mongolia. Haka zalika, an kafa wa matafiya tantuna masu nau'o'i daban daban, inda ake samar musu shayin da aka yi da madara, da sauran abinci mai dandano irin na 'yan kabilar Tibet da ta Mongolia.

To, maddala, masu karatu, ziyararmu a bakin tabkin Qinghaihu a yau ke nan. Bari mu huta kadan. Sai mako na gaba war haka, za mu ci gaba da ziyararmu a nan kasar Sin. Tasallah ce ke yi muku ban kwana daga nan sashen Hausa na CRI.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China