in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kyakkyawar surar Sanya
2010-02-09 13:34:54 cri
Birnin Sanya na kasancewa kuriyar kudu ta tsibirin Hainandao na kasar Sin, shi birni ne na yawon shakatawa daya kacal a bakin yankin teku na kasar Sin. Wannan birni na Sanya da ake kiransa "Hawaii da ke gabashin duniya" na da ni'imtattun wurare mafi kyan gani a bakin teku a kasar Sin. Wasu na cewa, in ba a je birnin Sanya ba, to, ba za a fahimci kyan surar lardin Hainan sosai ba. Yau za mu je wannan karamin birnin da ke bakin teku, da zummar fahimtar kyan surarsa ta musamman, wanda matafiya na gida da na waje na kasar Sin suka mayar da shi tamkar aljannar hutuwa saboda hasken rana da rairayin bakin teku da kuma halayen musamman na yankin zafi.

Birnin Sanya na kasancewa yanki zafi. Matsakaicin zafin yanayi a wurin ya kai digiri 23 bisa matsayin centigrade a duk shekara. Babu tsananin zafi a lokacin zafi, haka kuma, ba tsananin sanyi a lokacin hunturu. A duk tsawon shekara, yanayi na da dadi ainun. A lokacin zafi, ana rana kadan da tsakar rana, amma da safe da kuma dare iska kan buga daga wajen teku, ana sanyi. A lokacin hunturu fa, ko da yake a kan yi fama da tsananin sanyi a arewacin kasar Sin, tare da fama da kankara mai laushi. Amma a birnin Sanya, babu sanyi ko kadan. Wannan shi ne daya daga cikin dalilan da suka sanya mutane suna son wannan birni. Game da wannan, Zhang Yu, wani mazaunin birnin Beijing da ke aiki a birnin Sanya, ya fahimta sosai, inda ya ce,"A da na taba karatu a kasar Rasha. Bayan da na dawo kasar Sin, na zabi Sanya ba tare da bata lokaci ba. Wannan birni na da kyau matuka! A Rasha, ana sanyi sosai har na tsawon watanni 10 tare da lokacin zafi na tsawon watanni 2 a duk shekara. Amma a nan Sanya, duk tsawon shekara lokacin zafi ne. Kuma babu tsananin zafi a nan. In ba a dade a tsaya a karkashin hasken rana kai tsaye ba, sai ana jin sanyi sosai a sakamakon bugawar iska daga wajen teku, kamar lokacin kaka. Ina son wannan birni sosai."

Birnin Sanya ya dogara da babban tsauni a arewa, yayin da yake fuskantar teku a kudu. Yana da layin teku na tsawon kilomita dari 2 ko fiye. Teku kan jawo hankalin mutanen da ke zaune a yankuna marasa mafitar teku kwarai da gaske, balle ma a ce tekun da ake iya gani a birnin Sanya. Xia Rong tana zaune a lardin Sichuan. A wannan karo, ta zo birnin Sanya tare da iyalinta domin more kallon teku. A hakika, tekun da suke gani a birnin Sanya bai bata rai ko kadan ba. A lokacin ziyararsu a birnin Sanya, kyakkyawar surar teku ta zame musu abun tunawa mafi kyau. Inda ta ce,"Abun da na fi jin dadin kallo shi ne teku. Ana iya ganin abubuwa a cikin karkashin teku mai zurfi. A lokacin da muke zaune a jirgin ruwa, muna iya ganin gindin teku. Wannan yana da kyan gani sosai. Ya yi kama da sararin sama. Da zarar ka iso nan, sai kana son ka shiga cikin teku domin yin wasa da ruwan, sai ka ceka shiga teku. Wannan ya ba ni mamaki ainun. A ganina, kai wa teku ziyara na iya sanya ka kara jin dadi."

In an tabo zance kan tekun da aka samu a birnin Sanya, ba matafiya kawai ba, har ma da wadanda suke zaune a birnin Sanya su kan yi alfahari a kansa, saboda mutane da ba za su iya gajiya a fannin jin dadin kallon kyan surar teku ba har abada. Luo Weifu, mai shekaru 26 a duniya yana zaune a birnin Sanya tun lokacin da yake karami. Yana tafiyar da wani kulob din hawan keke. Ya san dukkan mashigan teku a birnin Sanya matuka. Ya gaya mana cewa,"Wuri mafi dacewa na jin dadin kallon kyan surar teku a birnin Sanya shi ne mashigin teku na Jinmujiao. Tsayawa a wuri mai tsayi a babban tsauni, kana iya yin farin ciki matuka, saboda kyan surar teku da ka iya gani ta kori abubuwan bakin ciki daga cikin zuciyarka kwata-kwata."

A ganin Luo Weifu, baya ga kallon teku mai kyan gani da ido, mutane kan iya yin wasa da teku ta hanyoyi masu ban sha'awa. Mashigan teku da mutane ba safai su kan bi ba ya fi jawo hankalinsu. Inda ya ce,"Yanzu muna iya jin dadin yin wasa da teku ta hanyoyin zabi son ka. Mun zo bakin teku tare da tufafin yin nitso cikin teku da bututun numfashi da gilas. Mu kan yi nitso cikin teku. A mashigan teku da ba a raya su zuwa wuraren yawon shakatawa ba tukuna, ba a yi barna kan ni'imtattun wuraren da ke kasancewa a gindin teku ba, ta haka duwatsun teku na murjani suna da girma sosai, haka kuma, akwai kifaye da yawa, wadanda ba su jin tsoron mutane, har ma in mutane sun kusance su, ba su gudu. Suna da kyan gani sosai."

Duk wanda ya je birnin Sanya ziyara tabbas ne zai nuna wa wannan birni sha'awa. Baya ga hasken rana da rairayin bakin teku, yanayin gudanar da harkokin zaman rayuwa sannu sannu ita ma dalili ne da ya sa mutane ke son wannan birni. Zaman rayuwa a nan na iya sa jikin mutane ya sake sosai. Wadanda ke zaune a nan suna tafiya sannu sannu, ba su yi hanzari ko kadan ba. Dangane da wannan, a matsayinsa na wani mazaunin birnin Sanya, Luo Weifu ya yi mana karin bayani kamar haka,"Ana gudanar da harkokin zaman rayuwa sannu a hankali, ba a yi hanzari ko kadan ba a nan birnin Sanya. Mutane kan sha shayi tare da cin wasu abincin kwadayi. A manyan birane, mutane kan gudanar da harkokin zaman rayuwa da ayyuka cikin sauri. Birnin Sanya na da kanana. Titunan da aka hana zirga-zirgar motoci da sauran wuraren da suka fi wadata na kusa da matsugunai. Tsawon lokaci da mazauna wurin kan dauka domin zuwa yankunan kasuwanci ya kai tsawon mintoci 5 kawai. Shi ya sa a yawancin lokaci, ba mu yi hanzarin harkoki ba. A biranen Shenzhen da Guangzhou, mutane kan tafe cikin sauri. A birninmu, ba mu yi tafiya da maza maza ba, sai sannu a hankali. A lokacin hutu, mu kan saki jikinmu."

Wannan gaskiya ne. Sakin jiki da aka samu a birnin Sanya ba safai a kan iya samun irinsa a sauran wurare ba. Mazauna wurin kan ce, "mu sha shayi tare in muna da lokaci." Su kan sha shayi tare da cin abubuwan kwadayi masu dandano da yamma. A ganin mazauna birnin Sanya, ba a iya kwatanta abubuwa masu farin ciki da shan shayi tare da abokan arziki da dangogi a kewayen teburorin shayi ba. Ta haka, har kullum in sun sami lokaci, su kan sha shayi.

Mutane da yawa sun bar manyan birane masu wadata, sun je birnin Sanya, saboda sun riga sun yi rashin hakuri da hayaniyar birane. Sun fi Alla-Alla wajen jin dadin zaman rayuwa mai kwanciyar hankali. A birni na Sanya, suna iya jin dadin shan shayi cikin kwanciyar hankali, da yin hira kan kome da kome, har ma suna kasancewa cikin shiru tare da rasa lura da kome

Ko da yake birnin Sanya karami ne, amma ya kan jawo hankalin mutane sosai da sosai. A nan, ana iya samun hasken rana mafi kyau da iska mafi ni'ima da teku mafi kyan gani. Mazauna birnin na da kirki da kyakkyawar halayya. Mutane kan iya jin dadi saka jiki a nan. A takaice dai, ga alama mutane kan so wannan birni, har ma ba su so su bar shi.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China