
Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 30 da kulla huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Zimbabwe. Domin taya murnar wannan muhimmiyar shekara, dukkan ma'aikatan ofishin jakadancin kasar Sin da ke kasar Zimbabwe sun kwashe kusan tsawon wata guda domin koyon rera taken kasar Zimbabwe da harshen Shona na wurin.
A cikin ofisoshin jakadancin kasashe daban daban da ke kasar Zimbabwe, ofishin jakadancin kasar Sin shi ne ofishin farko da ya koyi rera taken kasar Zimbabwe da harshen Shona. A karo na farko, ya nuna gwaninta ne a wannan fanni a 'yan kwanakin da suka gabata yayin da ya shirya biki don manyan jami'an Jam'iyyar ZANU-PF da ke kan karagar mulkin kasar Zimbabwe, wanda ya samu karbuwa kwarai da gaske. 'Yan Jam'iyyar ZANU-PF sun nuna yabo sosai ga 'yan diplomasiyya na kasar Sin, cewar sun nuna zummar karbar al'adun gargajiya na wurin da kuma yin cudanya tare da 'yan kasar Zimbabwe sosai a fannin al'adu.

