A ranar 8 ga wata, Ad Melkert, wakilin musamman mai kula da harkokin Iraqi na babban sakataren MDD ya ba da sanarwar yin Allah wadai da lamarin harbe 'yar takarar kasar Iraqi a ran 7 ga wata.
A cikin sanarwar da rukunin ba da tallafi ga kasar Iraqi na MDD ya bayar, Melkert ya yi gargadi cewa, ba a iya hakuri da kisar da aka yi wa wata 'yar takarar Iraqi a ran 7 ga wata a birnin Mosul ba, kuma ba a yarda da ayyukan karfin tuwo dake kawo barazana ga 'yan takara ko masu kada kuri'a ba ko kadan. Kuma ya ce, jama'ar Iraqi da 'yan takara, kamata ya yi, sun shiga ayyukan zabe a yanayin zaman lafiya.
An labarta cewa, Suha Abdulla al-Jaralla, 'yar takara ta rukunin Sunnis dake da shekaru 36 a duniya wadda ke neman samun kujera a majalisar kasar Iraqi, an harbe ta a ran 7 ga wata da dare a Mosul babban birnin lardin Nineveh dake arewacin kasar Iraqi.(Amina)

