Jia Qinglin yana fatan masu bin addinai da su kiyaye zaman lafiya da zaman karko don sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar

A ran 8 ga wata, a birnin Beijing, yayin da shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin Jia Qinglin ya yi shawarwari tare da masu bin addinai, inda ya bayyana cewar yana fatan kungiyoyin addinai daban daban da su yi hadin gwiwa sosai da jama'a masu bin addini don ba da hidima ga sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki da kiyaye dangantakar da ke tsakanin kungiyoyin addinai daban daban da kiyaye zaman lafiya da zaman karko.
Jia Qinglin ya kara da cewa, a shekarar 2009, an samu sakamako mai kyau a fannin gudanar da ayyukan addinai. Kungiyoyin addinai daban daban na Sin sun yaki da ayyukan yin tsolma biki cikin harkokin gidanmu da kungiyoyin kasashen waje suka yi ta hanyar addinai, musamman a fuskantar tashe-tashen hankali da aka samu a birnin urmuzi a ran 5 ga watan Yuli na shekarar bara, kungiyoyin addinai sun yi hadin gwiwa tare da gwamnatin Sin da jam'iyyar kwamnis ta kasar Sin, don kiyaye zaman lafiya da zaman karko da babbar moriyar jama'ar Sin.(Abubakar)