in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kawo karshen taron manufofin tsaro na Munich a karo na 46
2010-02-08 09:39:12 cri

A ran 7 ga wata, a birnin Munich dake kudancin kasar Jamus, an kawo karshen taron manufofin tsaro na Munich a karo na 46.

A gun taron dandalin tattaunawa mai taken "Nan gaba na NATO: manyan tsare-tsare da ayyuka" da aka yi a ran nan, babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen ya bayyana cewa, idan kungiyar NATO ta yi shirin kiyaye tsaron kasashe mambobinta, dole ne ta samu sauyi, kuma za ta zama wata cibiyar da kasashe mambobin kungiyar da sauran kasashen duniya za su yi shawarwari kan batun tsaron kasashen duniya tare. Mista Rasmussen ya jaddada cewa, kamata ya yi kungiyar NATO ta bunkasa dangantakar dake tsakaninta da Rasha da Sin da kuma India da dai sauransu.

Wannan shi ne karo na farko da ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya halarci dandalin tattaunawar manufofin tsaro kamar haka. Kuma a gun bikin bude taron da aka yi a ran 5 ga wata, mista Yang ya ba da jawabi mai suna "Kasar Sin da duniya dake samun sauye-sauye", inda ya bayyana matsayin kasar Sin kan manyan batutuwan zaman lafiya da kwanciyar hankali na duniya da ake fuskanta a halin yanzu.(Asabe)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
11:00 - 14:00 UTC Shirin Rana
Shiri na Yau Shiri na Jiya
15:00 - 18:00 UTC Shirin Yamma
Shiri na Yau Shiri na Jiya
16:30 - 17:30 UTC Shirin Maraice
Shiri na Yau Shiri na Jiya
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China