in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ayyukan soja da za a gudanar a kudancin kasar Afghanistan za su kyautata halin tsaro na kasar
2010-02-08 09:34:35 cri

A ran 7 ga wata, babban kwamandan sojojin Amurka dake a kasar Afghanistan Stanley McChrystal ya bayyana cewa, ayyukan soja da za a gudanar a jihar Helmand dake kudancin kasar Afghanistan za su bayyana wa jama'ar kasar Afghanistan cewa, gwamnatin kasar Afghanistan tana fadada wuraren da take iya kiyaye zaman lafiya.

A wannan rana a birnin Kabul, Mr McChrystal ya gudanar da wani taron manema labaru, inda ya ce, ayyukan soja da za a gudanar za su mai da hankali kan hadin gwiwar dake tsakanin sojoji da jama'a, ba ma kawai za a kyautata halin tsaro a wannan yanki a nan gaba ba, hatta ma za a inganta karfin gwamnatin kasar Afghanistan a fannin aiwatar da ayyukanta.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
11:00 - 14:00 UTC Shirin Rana
Shiri na Yau Shiri na Jiya
15:00 - 18:00 UTC Shirin Yamma
Shiri na Yau Shiri na Jiya
16:30 - 17:30 UTC Shirin Maraice
Shiri na Yau Shiri na Jiya
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China