
A ran 7 ga wata, sojojin kasar Lebanon sun bayar da sanarwar cewa, a ran nan, sojojin jiragen ruwan kasar sun gano gawawwaki 8 da suka rasa rayukansu sakamakon hadarin jirgin saman Habasha a watan jiya.
A cikin sanarwar, an ce, an yi amfani da jirgin ruwa na sojojin wajen sufurin gawawwakin zuwa sansanin sojojin, daga baya an kai wadannan gawawwaki a wani asibiti na birnin Beirut za a yin binciken gawawwakin don tabbatar da asalinsu.
Kuma a cikin sanarwar, an kara da cewa, za a ci gaba da gudanar da aikin kwashe gawawwaki, don kwashe sauran gawawwaki da akwati mai dauke da bayani wato bakin akwati.Kafin haka, sojojin kasar Lebanon sun taba sanar da cewa, a ran 7 ga wata, sun samu wani akwati mai dauke da bayani na jirgin saman.(Abubakar)

