
A ran 7 ga wata da dare, gidan talabijin na kasar Iran ya ba da labari cewa, a ran nan shugaban kungiyar nukiliya ta kasar Iran Ali Akbar Salehi ya bayyana cewa, daga ran 9 ga wata, Iran za ta fara ayyukan dake shafar sarrafa Uranium mai ingancin kashi 20 cikin dari.
Labarin ya ruwaito mista Salehi na cewa, a ran 8 ga wata, kasar Iran za ta gaya wa hukumar kula da harkokin nukiliya ta duniya wato IAEA shirinta na sarrafawa Uranium mai ingancin kashi 20 cikin dari, kuma za ta fara aikin daga ran 9 ga wata.
A ran 7 ga wata, shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadi Nejad ya ce, ya bukaci mista Salehi ya fara ayyukan dake shafar sarrafa sinadarin Uranium, amma kuma Iran tana son yin shawarwari kan batun yin cinikayyar makamashin Uranium. (Asabe)

