Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na kasar Angola ya bayar, an ce, shugaba Dos Santos ya yi bayani a gun bikin sa hannu a ran nan, cewar sabon tsarin mulkin kasar Angola ya fara aikinsa, wannan wani muhimmin lokaci ne a tarihin kasar, wanda ke sake sheda ci gaban kasar a fannin samun demokuradiyya. Sabon tsarin mulkin kasar kuma yana nuna cewa, jama'ar kasar Angola na iyar warware matsalolinsu bisa karfin kansu ba tare da samun wnai taimako daga waje ba. Kuma ya yi kira ga dukkan jama'ar kasar da su nuna girmamawa ga wannan tsarin mulkin kasar.(Kande Gao)

